Yadda kamfanonin layin waya suka kulle layuka miliyan 40 saboda Lambar ’Yan Ƙasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Sama da layukan waya miliyan 40 ne kamfanonin sanadar na MTN, Airtel, Glo suka kulle a ƙarshen mako biyo bayan ƙarewar wa’adin ranar 28 ga Fabrairu, 2024 da Hukumar Sadarwa ta Nijeriya ta bayar na tilasta wa masu amfani da layuka haɗawa da Lambobin Shaidar Ɗan Ƙasa, NIN.

Hakan ya nuna an samu ƙaruwar miliyan 28 daga layukan waya miliyan 12 da aka fara shirin kullewa, biyo bayan umarnin NCC.

A cikin sanarwar Disamba 2023, NCC ta buƙaci kamfanoin da su toshe layukan da ba a haɗa su da lambar NIN na masu su ba a ranar 28 ga Fabrairu, 2024.

A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne Daraktan Hulɗa da Jama’a na Hukumar NCC, Reuben Mouka, ya yi watsi da tsawaita wa’adin, yana mai gargaɗin cewa za a ci tarar kamfanonin sadarwa da suka gaza aiwatar da wa’adi.

Shugaban ƙungiyar dillalan sadarwa ta Nijeriya, Gbenga Adebayo, ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai cewa za su hana layukan sadarwa miliyan 12 sakamakon wannan umarni.

Sai dai a ranar Lahadin da ta gabata, shugaban ALTON ya bayyana cewa adadin layukan da aka kulle su ya haura miliyan 40.

A wani cigaban dai, a ranar Litinin ɗin da ta gabata ne Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) ta bayyana dalilin da ya sa aka kulle wasu masu amfani da layukan sadarwa duk da sun haɗa da Lambobin Shaidar Ɗan Ɗasa (NIN).

Mai magana da yawun NCC, Reuben Muoka, ya ce “an yi hakan ne saboda wataƙila ba su samu ingantaccen takardar shaidar NIN ba”.

“Har yanzu akwai wasu masu amfani da lambar NIN da NIMC ba ta tantance su ba kuma waɗanda kuma dole ne a gyara su,” inji shi.

Da yawa daga cikin masu amfani da layin sun koka da cewa a baya sun haɗa layukan su da lambar NIN shekaru da suka gabata amma an kulle masu layuka, inda jami’in hukumar NCC ya ce an yi haka ne saboda bayanan da ke cikin NIN bai yi daidai da abin da kwastomomin suka yi rajista ba.

Ya ce masu amfani da layin za su ziyarci ofisoshin sadarwar layukan su don tabbatar da lambar NIN ɗin su ya yi daidai da bayanan layukansu.