Rikicin siyasar Ribas: A shirye nake na sauka daga kujerar gwamna – Fubara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamna Sim Fubara na Jihar Ribas ya bayyana aniyarsa ta barin kujerarsa domin samun dorewar zaman lafiya a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da AIT a ranar Alhamis, 7 ga Maris, 2024.

A cewarsa, babu wata sadaukarwa da ta zarce shi da zai biya domin samun nasarar jihar.

Fubara ya ci gaba da cewa akwai abubuwan da zai iya yi waɗanda za su haifar da “rikicin gaba ɗaya”. Duk da haka, ikonsa na kamewa ko da yana da iko.

A yayin tattaunawar, Fubara ya ce, “Babu wata sadaukarwa da za ta kai ni in biya don samun nasarar wannan gwamnati.

“Kuma dalili mai sauƙi ne, ba soyayyar siyasa ba ce, ba don ina son samun wani tagomashi daga kowa ba, sha’awata da ƙaunar jiharmu ta gaskiya ce.

“Idan barin wannan matsayi shi ne abin da nake buƙata ko kuma abin da ake buƙata don samar da zaman lafiya a jihar, zan iya cewa ma ku mutane ku zo ku ɗauka. Ba game da ni ba ne. Ya kamata mutane su gane cewa tabbas zan tafi amma jihar Ribas za ta ci gaba da zama.

“Ni ne gwamna, ko mene ne, akwai abubuwan da zan iya yi kuma da an yi rikici gaba ɗaya. Amma ikon ku na kamewa yayin fuskantar rikici ko da kuna da ikon yin abubuwa shine dattaku.”

Idan dai za a iya tunawa Fubara da tsohon gwamnan jihar, yanzu haka ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, sun tsunduma cikin rikicin siyasa sakamakon savanin siyasa.

Wutar rikicin siyasa a Ribas a cikin watanni biyun da suka gabata ya kai matuƙa, lamarin da ya haifar da tashin hankali da fargaba kafin shiga tsakani da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi.

A cikin rikicin, an yi zargin Wike ya buƙaci wani kaso na kuɗaɗen shiga na Ribas, iƙirarin da ya musanta.

Akwai kuma yunƙurin da majalisar dokokin jihar ta yi na tsige gwamnan.

An kai harin bam a harabar Majalisar, inda Wike ya zargi Fubara da kitsa lamarin.

Haka kuma ‘yan majalisar dokokin jihar ashirin da bakwai masu biyayya ga Wike sun sauya sheƙa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a yunqurin tsige gwamnan.