Na gamsu da yadda Kwastom suka daina wawashe kayan ‘yan kasuwa – Sarkin Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya nuna gamsuwarsa bisa yadda aka samu fahimtar juna tsakanin ‘yan kasuwa da jami’an Hukumar Fasa-ƙwauri ta Ƙasa wajen sakar musu mara ba tare da barin shiga kasuwanni ana kwashe musu kaya.

Sarkin ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi baƙoncin Shugaban hukumar na ƙasa, Bashir Adewale Adeniyi a fadarsa.

Ta cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na masarautar Kano, Abubakar Balarabe Kofar Na’isa, ya aike wa Manhaja ya ce, Alhaji Aminu Ado Bayero wanda ya ce a baya sun sha karɓar ƙorafe-ƙorafe na yan kasuwa bisa yadda jami’an hukumar kwastam suke shiga kasuwanni su kwashe musu kaya wanda a yanzu abun ba haka yake ba.

Kazalika, Basaraken ya buƙaci Babban Kwantirolan na ƙasa da idan za su raba kayan abinci da su duba mabuƙata wajen raba musu kayan, yana mai cewa Masarautar Kano a shirye take ta bayar da goyon baya da hadin,

A nasa jawabin, Bashir Adewale Adeniyi ya ce sun zo fada ne domin neman tabarrukin Sarki da shawarwari a kan ayyukansu.

Bashir ya samu rakiyar shugabn hukumar shiyyar Kano da Jigawa, Dauda China da kuma wasu manyan jami’an hukumar.

By Editor