Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana yadda tsohon shugaban bankin Access, Herbert Wigwe ya ba shi gudunmawa a lokacin da aka sauke shi daga karagar mulki.
Yayin da yake jawabi a taron nuna alhinin rasuwar tsohon jami’an bankin da ya rasu a wani hatsarin jirgi tare da iyalinsa a Amurka, sarkin Kanon na 14 ya ce ya kaɗu matuƙa da jin labarin rasuwar mista Wigwe wanda ya taka rawar gani a rayuwarsa.
“Na yi tunanin zan riga mista Herbert rasuwa. duka mun san irin kirkinsa, da biyayyarsa,” inji Muhammadu Sanusi ll, lokacin da yake jawabi yana shasshakar kuka.
Ya ce, tsohon jami’an bankin na Access ya yi masa alƙawarin ba shi goyon baya a lokacin da aka sauke shi daga karagar mulki.
Tsohon gwamnan CBN ɗin ya ce a lokacin har jirgin sama Herbert ya tanadar masa don ɗaukarsa daga Kano zuwa Legas.
“A lokacin da na samu matsala a Kano, wata shida kafin a sauke ni, na kira shi na faɗa masa halin da ake ciki, sannan na ce masa, “Herbert na san irin ƙoƙarin da kake yi wajen magance wannan matsala, amma na san saukeni za a yi.
“Sai ya ce min, mai martaba, kada ka damu. duk abin da ya faru kar ka damu muna tare da kai. A ranar da na ji sanarwa a radiyo cewa an saukeni, sai na kira shi na ce masa ina son zuwa Legas.
“An yi sanarwar da misalin karfe 9:00 na safe, zuwa da rana Herbert ya tanadar mini da jirgi a filin jirgin sama na Kano, sai dai a lokacin an tsara cewa za a kaini zaman gudun hijira nashekaru masu yawa, daga nan sai na saka iyalina cikin jirgin tare da tura su Legas, ban yi waya da shi ba, amma ya tarbe su tare da sauke su a otel, kafin daga baya ya samar musu da matsuguni, inda suka kwashe watanni suna zaune kafin na dawo Legas don cigaba da zama tare da iyalina.”
Muhammdu Sanusi ll ya kuma ce Herbert ya yi masa alƙawarin ɗaukar nauyin tafiye-tafiyensa bayan komawa Legas da zama.
