Tsaro: Shugaban Jami’ar Bayero ya buƙaci a samar da kuɗin katange jami’ar

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban Jami’ar Bayero da ke Jihar Kano, Farfesa Sagir Abbas, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta saki kuɗaɗen da aka ware domin katange jami’ar saboda matsalolin tsaro da ake fama da su.

Farfesa Abbas ya bayyana halan ne yayin taron taro karo na 38 da aka gudanar a Jami’ar Bayero a Kano.

Abbas ya jaddada muhimmancin waɗannan kuɗaɗe, inda ya bayyana cewa, duk da cewa akwai kaso na farko a cikin kasafin kuɗin tarayya na shekarar 2023, daga baya kuma an cire shi a shekarar 2024, wanda hakan ya sa jami’ar ta shiga cikin mawuyacin hali.

“Tare da kusan ma’aikata 50,000 da ɗalibai a Sabon Harabar mu, rashin katanga yana haifar da babban barazanar tsaro. Muna roƙon Gwamnatin Tarayya da ta dawo da tanadin kasafin kudin domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma,” Abbas ya jaddada.

Ya bayyana irin matakan da jami’ar ta ɗauka, waɗanda suka haɗa da tura jami’an soji, ’yan mafarauta, da kuma jami’an tsaron gandun daji domin inganta tsaro, musamman cikin dare abin a yaba ne.

Abbas ya kuma yi tsokaci kan ƙalubalen da ke tattare da rashin katanga a sabon harabar, yana mai jaddada buƙatar gwamnati ta shiga lamarin cikin gaggawa.

Baya ga magance matsalolin tsaro, taron taron ya yi nasarar ba mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau Jibrin da kuma shugaban bankin cigaban Afirka Dr. Akinwumi Adesina digiri na girmamawa bisa ga irin gudunmawar da suka bayar wajen cigaban ƙasa da taimakon al’umma.

Bikin ya nuna nasarorin da ɗalibai 180 da suka kammala karatun digiri na farko, masu digiri 370 da suka samu digirin digirgir (PhD), da kuma masu digiri 3,770, tare da waɗanda suka samu digirin farko su 11,284 a ɓangarori daban-daban.