Ina farin ciki da matakan da gwamnatin Tinubu ke ɗauka – Buhari

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana farin ciki da irin salon mulkin gwamnati shugaba Tinubu duk da halin matsin rayuwa da taɓarɓarewar tattalin arziki a Nijeriya.

Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya kai masa ziyarci a Daura, Jihar Katsina.

Shettima ya ce, Gwamnatin Tarayya a ƙarƙashin jagorancin shugaba Bola Tinubu ba za ta bar wani abu da zai kawo cikas a yunƙurinta na kare rayuka da dukiyoyin ’yan Nijeriya ba.

Mataimakin shugaban Nijeriya ta cigaba da cewa, ya sha alwashin cewa gwamnati mai ci za ta yi amfani da albarkatun da ake da su don yaƙi da rashin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Ƙasa.

Yayin da yake nuna godiya ga mataimakin shugaban ƙasa Shettima kan ziyarar, tsohon shugaban ƙasa Buhari ya yaba wa gwamnati mai ci bisa ƙoƙarin da take yi na daidaita tattalin arzikin ƙasar.

Ya ce, “Na yi matuƙar farin ciki da yadda suka iya daidaita lamura kuma sun ci gaba da nuna damuwa da halin da ‘yan Nijeriya da kre ciki. Na yi matuƙar farin ciki da ƙwazonsu.”

A halin da ake ciki dai, ‘yan Nijeriya da dama na cikin mawuyacin hali biyo bayan cire tallafin man fetur da kuma faɗuwar darajar Naira a ƙasar.

Manufofin sun qara tsadar kayayyaki da kayan abinci. Duk da cewa Asusun Ba da Lamuni na Duniya ya yaba wa Tinubu kan jajircewarsa wajen yanke shawarwarin tattalin arziki masu tsauri da magabata suka kasa yankewa, amma da dama daga cikin ’yan Nijeriya na caccakar gwamnatin da cewa tana adawa da talakawa.

Sakamakon haka, an yi zanga-zanga da wawason kayan abinci a wasu jihohin don nuna adawa da halin ƙunci da tsadar rayuwa da ba a tava yin irinsa ba.