Ku dawo da kuɗin tallafi Korona – Majalisar Wakilai ga kamfanonin jiragen sama

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kwamitin Kula da Harkokin Gwamnati na Majalisar Wakilai ya bayar da wa’adin mako guda ga dukkan kamfanonin jiragen sama masu zaman kansu a ƙasar nan da su yi lissafin yadda suka kashe zunzurutun kuɗi har Naira Biliyan 4 da Gwamnatin Tarayya ta ba su don magance cutar COVID-19 ko kuma su dawo da kuɗaɗen.

Kwamitin wanda ɗan jam’iyyar PDP daga jihar Osun, Bamidele Salam ya jagoranta, ya bayar da wa’adin ne a ranar Juma’a a wajen ci gaba da zaman bincike kan zargin karkatar da kuɗaɗen shiga a tsakanin ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya.

An ruwaito cewa kwamitin na binciken sama da manyan ma’aikatu biyar bisa zargin karkatar da kuɗaɗen shiga.

Kwamitin ya ce, “Dukkanin kamfanonin jiragen sama masu zaman kansu da suka karɓi tallafin COVID-19 da aka ware don tallafawa ɓangaren sufurin jiragen sama, za su mayar da kuɗaɗen da aka ware wa baitul malin gwamnatin tarayya cikin mako guda idan har suka kasa bayar da hujjar yadda aka kashe kuɗaɗen cikin hikima.”

Kwamitin ya koka da cewa, duk da bayyanar su, yawancin kamfanonin jiragen sama da masu ruwa da tsaki a masana’antu da suka haxa da Aero Contractors, Azman da wasu daga ma’aikatar sufurin jiragen sama da raya sararin samaniya ta tarayya, sun kasa gamsar da ‘yan majalisar kan yadda aka kashe kuɗaɗen da aka ba su wajen gudanar da ayyukan daƙile tasirin cutar COVID-19.

Da yake mayar da martani kan abubuwan da aka gabatar, wani mamba a kwamitin kuma tsohon matuin jirgi na rundunar sojojin saman Nijeriya Ojuawo Adeniyi daga jihar Ekiti, ya yi zargin cewa ayyukan da kamfanonin ke yi na yin amfani da su ne kawai a lokacin gudanar da harkokin sufurin jiragen sama na yau da kullum.

Daga baya, ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Calabar Municipal/Odukpani, jihar Cross River, Akiba Bassey, ya gabatar da buƙatar a maido da Naira Biliyan huɗu ga asusun tarayya idan kamfanonin jiragen sama sun gaza bai wa kwamitin cikakken bayanin yadda suka kashe kuɗin tallafin.