Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wani ƙwararren ma’aikacin da ya yi nazarin takardun binciken da hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa, EFCC, Bamaiyi Haruna, a ranar Alhamis, ya ce, binciken da aka yi kan takardun da aka yi amfani da su wajen fitar da zunzurutun kuɗi har Dala Miliyan 6.2 daga Babban Bankin Nijeriya (CBN) a watan Fabrairun 2023 ya nuna cewa jabu ne sa hannun tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari akansu.
Hukumar EFCC ta yi zargin cewa a ranar 8 ga Fabrairu, 2023, tsohon Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya haɗa baki da wani mai suna Odoh Ocheme, don su karɓi Dala Miliyan 6.2m daga Bankin CBN, yana mai ƙaryar cewa, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boos Mustapha, ya buqaci hakan a cikin wasiƙar mai kwanan wata 26 ga Janairu 2023 tare da Ref No. SGF.43/L.01/.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta kuma yi zargin cewa, Emefiele, a watan Janairun 2023, ya yi jabun takarda mai taken: “RE: PRESIDENTIAL DIRECTIVE ON THE FORIGN ELECTION OBSERVER MISSIONS,” wato ‘Umarnin Shugaban Qasa Akan Masu Sa Ido Kan Zaɓe daga Ƙetare’, mai kwanan wata 26 ga Janairu 2023 tare da lamba (Ref No.) SGF.43/L.01/201.
A ranar da aka ɗage zaman na ƙarshe, tsohon Boss Mustapha ya bayyana cewa, takardun ba su fito daga tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ko ofishinsa a matsayin Sakataren Gwamnati ba.
Mustapha ya kuma shaida wa kotun cewa, Gwamnatin Tarayya ba ta da wata alaƙa da masu sa ido kan zaɓe na ƙasashen waje.
Mai Binciken Kuɗi Haruna, wanda shine shaidar masu gabatar da ƙara a kan lamarin, ya bayyana cewa, an tantance sa hannun Buhari da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya na gaskiya da waɗanda ke jikin takardun, inda suka gano ba ɗaya ba ne.
Ya ce, “a ƙarshe daga binciken ya nuna cewa, takardun da ake taƙaddama a kai sun nuna shaidar jabu da kwafi kamar yadda tsarin motsi da samar da sa hannun alƙalami da fasahar aiwatar da su ya bambanta da na samfurin sa hannun A zuwa A2 da B zuwa B1.
“Siffar da samuwar sa hannun da aka yi wa alama X da samfurin sa hannu mai alamar B zuwa B1 an gano sun bambanta dangane da motsin alƙalami, ƙwarewar aiwatarwa, samuwar maɗauki, akwai halayen mutum ɗaya. Wannan ya tabbatar da cewa marubucin sa hannun samfurin mai lamba B zuwa B1 bai yi la’akari da sa hannun Buhari ba a kan takardar da ake taƙaddama a kai mai alamar X.
“Haka kuma, sigar da samuwar sa hannu da aka yi jayayya mai lamba X1 da sa hannu na A2 suma an gano sun bambanta dangane da motsin alƙalami bugun farko da na ƙarshe, samuwar maɗauki, kasancewar rawar jiki, da halayen mutum ɗaya. Wannan kuma ya tabbatar da cewa marubucin sa hannun samfurin mai lamba A2 bai iya sa hannun Boss Mustapha ba a kan takardar da aka samu saɓani mai lamba X1.”
Lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo (SAN), ya nemi kotu da ta gabatar da rahoton bincike mai kwanan wata 25 ga watan Janairu, 2024, da sauran takardun da aka maƙala a matsayin nuni.
Mai shari’a Hamza Muazu ya bayyana hakan a fili kuma ya nuna musu FDE.
A yayin da ake yi masa tambayoyi, Burkaa ya tambayi ta yaya kotu za ta tantance ko sa hannun biyu na da kamanceceniya ko kuma savanin haka.
Shaidan ya buƙaci kotun da ta dogara da rahoton.
Da aka tambaye shi ko an yi nazarin sa hannun Emefiele, sai ya ce a’a.
Har ila yau aka tambaye shi ko jami’an EFCC sun gabatar da kayan da aka tantance, Haruna ya ce, “Hukumomin EFCC sun miƙa buƙatar ga sashen.”
Daga bisani an ɗage ci gaba da sauraren ƙarar har zuwa ranar 11 ga Maris.
