An daina sauya wajen hidimar ƙasa – Shugaban NYSC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban Masu Yi Wa Ƙasa Hidima, NYSC, Birgediya Janar Yusha’u Ahmed, ya ja hankalin masu hidima da su rungumi wuraren da ake tura su tare da bayar da tasu gudunmawar wajen cigaban jihohin da aka ba su.

Da yake zantawa da masu hidima na Batch A Stream 1 a yayin bikin shiga sansanin wayar da kai na jihar Anambra, Ahmed ya jaddada muhimmancin mutunta tsarin hidimta wa ƙasa tare da ba da fifiko ga tsaron su.

Ya ba da shawarar cewa, “Ku kasance cikin kwanciyar hankali da juriya yayin da ku ke ƙara kima ga yankunan da aka tura ku. 

Tsaronka shi ne damuwarmu, amma babu wanda zai iya kiyaye ka fiye da kanka. Ku ɗauki lokaci don karanta umarnin da ke cikin littafinku kuma ku bi su daidai.”

Ahmed ya ƙara jaddada muhimmancin koyon sana’o’i da bunƙasa harkokin kasuwanci a cikin shirin na NYSC, inda ya buƙaci masu hidima da su yi amfani da shirin domin dogaro da kai da samar da ayyukan yi bayan shekarar hidimarsu.

Ya ce, “An ƙirƙiri koyon sana’o’i ne ga masu hidima domin amfanin kansu. Gwamnatin Tarayya ta ƙuduri aniyar tallafawa da bai wa matasa damar tsayawa da ƙafar su. Yawancin magabata a NYSC sun amfana da irin wannan damar kuma yanzu sun kasance masu dogaru da kansu.”

Shugaban NYSC, wanda Igwe Joel Egwuonwu, sarkin gargajiya na al’ummar sansanin ya karrama shi da sarautar Dike Ora I na Umuawulu, ya nanata muhimmancin mutunta tsarin yankunan da suka karɓi baauncin, yana mai jaddada haɗin kai da ajiye bambancin ra’ayi.

Ya kuma yi alƙawarin cigaba da yin haɗin gwiwa da gwamnatocin jihohi domin inganta sansanonin, musamman ganin yadda ake samun ƙaruwar masu hidima da ake yaye wa daga jami’o’i duk shekara.

A ɓangare guda, Shugaban NYSC ya bukaci masu hidimta wa ƙasa su guji shiga harkokin siyasa.

Birgediya Janar Yusha’u Ahmed, Shugaban Hukumar Masu Yi Wa Ƙasa Hidima, NYSC ya jaddada muhimmancin haɓaka rayuwa ga matasa a shekarar hidimarsu.

Ya jaddada muhimmancin tasiri ga al’ummomin da suka karɓi baƙuncinsu tare da ƙarfafa su zuwa yankunan da aka tura su.

Ahmed ya bayyana damar da ake da shi na samun ƙwarewa da bunqasa harkokin kasuwanci a cikin shirin, inda ya buƙaci matasan da su neman hanyoyin dogaro da kai da kuma ba da gudunmawa ga cigaban ƙasa.

Bugu da ƙari, ya jaddada muhimmancin wayar da kan tsaro, sannan ya buƙaci matasan da su ɗauki tsaron lafiyarsu da muhimmanci tare da inganta haɗin kan aasa ta hanyar amfani da kafafen sada zumunta na zamani.

Ahmed ya nuna godiya ga Gwamnatin Jihar Sakkwato da Majalisar Sarkin Musulmi bisa goyon bayan da suke ba wa shirin NYSC.