‘Yan daba sun yi wa filin jirgin saman Haiti dirar mikiya

Kwana guda bayan da gungun ‘yan daba suka ɓalle manyan gidajen yari biyu a Haiti, a yau kuma sun farwa babban filin jirgin saman ƙasar da nufin karve iko da shi.

Wannan ta sa dole ƙasashen da ke maƙwaftaka da Haiti suka fara ƙarfafa tsaron kan iyakokin su don gudun fantsamar ‘yan dabar zuwa cikin su.

Faya-fayan bidiyo sun nuna yadda aka riƙa musayar wuta tsakanin jami’an sojoji da kuma ‘yan dabar sama da 500.

Har kawo yanzu filin jirgin saman na The Toussaint Louverture na kulle yayin da aka dakatar da duk wata zirga-zirga.

Ko a makon da ya gabata sai da ‘yan bindigar suka yi arangama da jami’an tsaro a filin jirgin, sai dai lamarin bai yi muni irin na yau ba, abinda ke ƙara jefa fargaba game da yiwuwar ‘yan dabar su ƙwace iko da filin jirgin.