Gwamnan Zamfara ya sha alwashin hukunta waɗanda suka kashe Sheikh Abubakar

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya lashi takobin hukunta waɗanda suka kashe Sheikh Abubakar Hassan Mada a jihar.

Wasu da ake zargin ‘yan banga ne suka kashe malamin a makon jiya a garin Mada, cikin Ƙaramar Hukumar Gusau, Jihar Zamfara.

Kakakin Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar ran Juma’a cewa, Gwamna Lawal ya ziyarci garin Mada don yi musu ta’aziyya kan rasuwar malamin, inda a nan ya yi sallar Juma’a a babban masallacin garin.

Ya ce, yayin da yake yi wa jama’a jawabi, Gwamna Lawal ya yi alƙawarin zai yi iya iyawarsa wajen tabbatar da an yi adalci game da kisan marigayin.

A cewar Gwamnan: “Na zo ne domin sake jaddada wa al’ummar garin Mada cewa za a yi adalci kuma za a hukunta waɗanda ke da hannu a kisan.

“Babu abin da za mu bari domin tabbatar da adalci kan kisan da aka yi Sheikh Abubakar. Za mu yi aiki ba dare, ba rana domin tabbatar an yi wa iyalan marigayin adalci.

“Ba na Gusau lokacin da abin ya auku, amma samun labari ke da wuya sai na tuntuɓi shugabannin hukumomin tsaro kan su yi abin da ya dace.

“Ba tare da ɓata lokaci ba ‘yan sanda suka soma gudanar da binci. Na rantse da Allah za a hukunta duk wanda aka samu da hannu cikin kisan,” in Lawal.