Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta musanta ikirarin sace fasinjoji 26 da aka yi a kan hanyar Gusau zuwa Sakkwato.
Rahotanni sun bayyana cewa, wasu gungun ‘yan bindiga sun tare hanya tare da garkuwa da masu ababen hawa. Sai dai ’yan sandan sun yi gaggawar mayar da martani tare da fatattakar ’yan bindigar, lamarin da ya maido da zaman lafiya a yankin.
Kakakin ‘yan sandan Yazid Abubakar ya bayyana cewa yayin da ‘yan bindigar suka tare hanyar, babu wani fasinja da aka sace. Ya kuma jaddada cewa ’yan sanda sun yi nasarar tarwatsa ’yan bindigar, tare da hana yin garkuwa da jama’a.
Abubakar ya buƙaci jama’a da su yi watsi da bayanan da ba su dace ba, ya kuma ba da tabbacin cewa an ɗauki matakan hana afkuwar irin wannan lamari a nan gaba.
A wani labarin kuma wasu ’yan bindiga a jihar Zamfara sun kashe mutane tara tare da yin garkuwa da wasu 27 a ƙauyen Makera da ke Ƙaramar Hukumar Talata-Mafara.
Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun mamaye ƙauyen, inda suka riƙa harbi ba ƙaƙƙautawa tare da yin awon gaba da mutane da dama.
