Da Ɗumi-ɗumi: Kotu ta ba da belin tsohon Gwamnan Kwara kan N50m

Daga BASHIR ISAH

Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Ilorin, Jihar Kwara kuma ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Evelyn Anyadike, ta ba da belin tsohon Gwamnan Jihar Kwara, Alh AbdulFatah Ahmed.

Kotu ta ba da belin ne bisa sharuɗɗa da suka haɗa da biyan Naira miliyan 50 ga kotu da shaida wanda ya mallaki fili aIlorin da sauransu.

Ana da ran tsohon gwamnan ya ci gaba da zama a hannun EFCC har zuwa lokacin da zai cika sharuɗɗan.