Tinubu ga ’yan Nijeriya: Ba zan yi gaggawa wajen sake fasalin ƙasa ba

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa gwamnatinsa za ta sake fasalin ƙasar kamar yadda ya yi alƙawari tun da farko, amma ya lura cewa dole ne a aza harsashi mai kyau.

Tinubu ya bayar da wannan tabbacin ne a wata ziyarar da ya kai wa jagoran ƙungiyar siyasa da zamantakewar al’ummar Yarabawa ta ƙasa, Afenifere, Pa Reuben Fasoranti, a Akure, Jihar Ondo ranar Laraba.

Bayan ganawar sirri da wasu zaɓaɓɓun shugabannin ƙungiyar, sakataren yaɗa labaran ƙungiyar na kasa, Mista Jare Ajayi, ya ruwaito shugaban qasar na tabbatarwa ‘yan Nijeriya cewa zai sake yin garambawul amma akwai buƙatar a samar da wasu tsare-tsare.

A yayin da yake ambato shugaban ƙasar, Ajayi ya ce: “Akan batun sake fasalin ƙasa, shugaban ƙasar ya ce yana sane da buƙatar sake fasalin Nijeriya amma sai an shimfiɗa kyakykyawan harsashi kafin a kawo gyara ta yadda idan aka yi gaggawar aiwatar da shi ba tare da ingantaccen tushe ba, sake fasalin zai iya rushewa nan da nan amma za a yi.

“Ya ce (Tinubu) ya ce a lokacin da ya yi rantsuwar mulki, shi (Tinubu) ya yi mubaya’a ga Nijeriya, cewa ya san abin da yake fuskanta.

“Ya (Tinubu) ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa ya fahimci gwagwarmayar kuma yana ƙoƙarin ginin da ba za a juya baya ba.

“Shugaban ya ce tsarin da yake ƙoƙarin samar da shi a Nijeriya ta fuskar tattalin arziki, zamantakewa da siyasa zai kasance irin wanda zai dawo da Nijeriya inda ya kamata.

“Akan wahalhalun da ‘yan Nijeriya ke fuskanta, shi (Tinubu) yana sane da irin raɗaɗin da ‘yan Nijeriya ke ciki, ya kuma ce nan ba da daɗewa ba, Nijeriya za ta shawo kan lamarin; wannan abu ne na ɗan lokaci. Ya ce irin manufofin da gwamnati ke aiwatarwa za su kawo mafita mai kyau ga ƙalubalen.

“Ya ce ‘yan Nijeriya su noma abincinsu. Cewa mu ci abincin da muke nomawa. Yin hakan zai yaye mu daga dogaro da abinci daga waje.”

Da yake mayar da martani, Pa Fasoranti ya ce: “Ayyukan da kuka yi ya zuwa yanzu sun nuna cewa kun fahimci cikakken nauyin aikin da aka ba ku wanda ke nuna wa al’ummar Nijeriya cewa gwamnati mai kyau za ta yiwu.

“A ƙasar Yarbawa, ba ma neman wata kulawa ta musamman ko wata fa’ida ta rashin adalci. Mun san ku namu ne, amma yanzu ku na duk ’yan Nijeriya ne. Al’ummar Nijeriya ne suka ba ku kyauta kuma Allah ya albarkace ku.

“Don haka mai girma shugaban ƙasa ya ci gaba da gudanar da mulki bisa adalci da jajircewa tare da tsoron Allah. Abin da muke tsammani ke nan, abin da muka san za ku yi ke nan.

“Kun san cewa tun bayan soke zaɓen shugaban ƙasa da aka yi a ranar 12 ga watan Yunin 1993, ‘yan ƙabilar Yarbawa ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar Afenifere ne ke kan gaba wajen yakin neman sake fasalin Nijeriya.

“Yanzu ya zama wajibi a gare ku ku magance wannan batu na sake fasalin tsarin mulki cikin jajircewa, adalci da kuma azama.

“Mun san ba za mu iya komawa baya ba, amma dole ne mu nemi makoma inda gasannin yanki za su fitar da mafi kyawu a ƙasarmu kamar yadda aka yi a lokacin jamhuriya ta farko.

“Saboda haka, muna neman Jamhuriyar Tarayya ta gaskiya wacce za ta nuna tsarin tarayya na kasafin kudi. Mun yi imanin sake duba taron Tsarin Mulki na 2014 zai taimaka muku wajen tsara kwas.

“Ga mutanen Kudu maso Yamma, sake fasalin tsarin yana da ma’ana mai muhimmanci. A yau, Nijeriya tana da mutane miliyan 200 wanda zai ninka nan da shekaru 25 masu zuwa, zuwa miliyan 400.

“Duk da haka, yankin Kudu maso Yamma na fuskantar bala’in gudun hijira daga sauran shiyyoyin ƙasar nan, ta yadda a cikin shekaru 25, idan aka ci gaba da tafiya a halin yanzu, yankin Kudu maso Yamma zai kasance gida mai kashi 50 cikin 100 na al’ummar Nijeriya.

“Muna buƙatar mu shirya don kada yankinmu ya mamaye ƙalubalen da ake shigo da su daga ƙasashen waje.

“Muna son kowane yanki na siyasa ya kasance yana da nauyi mai yawa na tsaro, samar da abinci da ci gaban ababen more rayuwa.

“Tun daga lokacin da aka cire tallafin man fetur da ake kashewa Nijeriya dala biliyan 10 duk shekara, gwamnatocin jihohi ke karɓar kaso mai tsoka daga asusun tarayya.

“Ya kamata mai girma shugaban ƙasa ya jawo hankalin gwamnonin da su bar wannan sauyi na arziki ga jahohin su yi ta tunani tun daga tushe domin rayuwa ta samu sauƙi ga al’ummarmu. Kada su saya wa jama’a shinkafa da dawa kawai.

“Ya Shugaba, na gode da wannan ziyarar. Kuna da haƙƙin zuriya don bauta wa Nijeriya da dukkan ƙarfinku da hikimarku.”

Tun da farko dai, Shugaba Tinubu, a ziyarar da ya kai Olowo na Owo, Oba Ajibade Ogunoye, domin jajantawa al’ummar jihar bisa rasuwar tsohon gwamnan, Mista Rotimi Akeredolu, ya ce shi (Akeredolu) ya bar wani giɓi da zai yi wuyar cikawa.

Tinubu ya ce: “Ya kamata wannan ra’ayin ya zaburar da mu mu yi rayuwa a kowace rana da manufa, mu cimma burinmu da azama, mu bar abin da zai zama abin tunawa.”

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana Akeredolu a matsayin mutum mai kare gaskiya mara tsoro a lokacin rayuwarsa, inda ya jajenta wa iyalansa da faran Allah ya ba su haƙurin rashi.

By Editor