‘Duk jam’ina da ya nemi cin hanci ku sanar da ni’ Tinubu ga ‘yan kasuwar Qatar

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga ‘yan kasuwa na ƙasa da ƙasa kan cewa kada su bai kowa cin hanci kafin gudanar da harkokinsu a Nijeriya, kuma duk wani jami’insa da ya nemi a ba shi cin hancin a kai ƙararsa.

Tinubu ya bayyana haka ne sa’ilin da yake jawabi a wajen taron Zuba Jarida na Nigeria-Qatar ranar Lahadi a Doha, Qatar.

A cewarsa, “Kada ku bai wa kowa cin hanci, kuma duk wanda ya karɓa ko ya nemi ku ba shi cin hanci, ku sanar da mu.”

Shugaban ya ƙara da cewa a shirye Nijeriya take don yin kasuwanci, kuma gwamnatinsa za ta ɗauki mataki a kan duk wanda ya yi ƙoƙarin cire wa masu zuba jari a ƙasar ƙwaron gwiwa.

Tinubu ya yi alƙawarin kawar da duk wani abu da zai haifar da cikas ga samun riba ga ‘yan kasuwar da suka yi nufin zuba jari a Nijeriya.

Ya shaida wa taron an bunƙasa tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya wadda ta kasance ƙasa mafi ƙarfin tattalin arziki a nahiyar Afirka.

Kazalika, Shugaban ya bai wa ‘yan kasuwar tabbacin samun zarafin ta’ammali da ofishin Shugaban Ƙasa ba tare da wata wahala ba a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso.

Ta bakinsa a wajen taron, “Na zo nan ne don ba ku tabbacin ingantattun sauye-sauyen da ke gudana a fannin tattalin arzikin Nijeriya, ku mance da duk abin da kuka ji a baya.

“Duk wata matsala ko cikas da wasunku suka fuskanta, wannan a baya ne, domin babu irin wannan matsala a gaba,” in ji shi.

By Editor