Ramadan: Ɗangote ya ƙudiri aniyar tallafa wa mabuƙata da kayan abinci

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Hamshaƙin mai arzikin nan Alhaji Aliko Ɗangote mai son tallafawa al’ummar ƙasar nan don sauƙaƙa musu daga halin matsin tattakin arzikin da ake ciki zai tallafawa mabuƙata da kayan abinci kyauta don yin azumin watan Ramadan cikin walwala.

Ɗiyarsa Hajiya Fatima Aliko Ɗangote ce ta bayyana hakan, yayin wani taron ganawa da ‘yan jaridu na Arewacin Nijeriya da ya gudana a birnin Kano.

Hajiya Fatima ta ce mahaifinta ya jima yana gudanar da ayyuka domin kyautata rayuwar al’ummar Jihar Kano, shi ya sa a wannan lokaci ya ƙudiri aniyar tallafawa mabuƙata da kayan abinci sakamakon halin qunci da matsin rayuwar da ake ciki.

Ga waɗanda ke bibiyar ayyukan jinƙai na Gidauniyar Ɗangote suna sane da yadda ake gudanar da ayyukan inganta rayuwar jama’a a asibitoci baya ga bayar da abinci ga mabuƙata tsawon shekaru.

By Editor