Uwargidan gwamnan Kebbi ta tallafa wa mata da Naira miliyan 10

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi

Uwargidan gwamnan Kebbi Hajiya Zainab Nasir ta tallafawa mata masu ƙananan sana’o’i da Naira milliyan goma a ƙarƙashin hukumar SMEDAN.

Uwargidan Gwamnan ta bayar da wannan tallafin ne a lokacin da take halartar taron Ramadan Funfair da ya gudana ranar Lahadi a babban ɗakin taro dake Shugaban Ƙasa wato Presidential Lodge dake cikin garin Birnin Kebbi.

Da take jawabi a wurin taron, uwargidan Gwamnan ta bayar da umarnin cewar dukkanin matan da suka halarci taron da sana’o’insu da a tabbatar sun samu wani kaso a cikin gudunmawar kuɗin da ta bayar.

Haka kuma ta yaba wa mata ‘yan kasuwar da suka baje hajojinsu a wurin taron akan yadda suka rage farashin kayansu domin samun sauƙin saye ga al’umma.

Haka kuma ta buƙaci mata ‘yan kasuwar da su cigaba da gudanar da kasuwancinsu har a gidajensu domin tabbatar da ɗorewar hulɗa da masu sayen sana’o’insu.

Haka kuma ta yi godiya ta musamman ga wacce ta shirya shirin Hajiya Maryam Bello Bala bisa yadda take taimakawa mata musamman masu ƙananan sana’o’i domin ganin sun cigaba samun sana’o’in dogaro da kai.

Kwamishiniyar Ilmin bai ɗaya a matakin farko wato Basic and Secondary Education, Dakta Halimatu Muhammad Bande, ta yi kira ga mata ‘yan kasuwar da su yi ƙoƙari su haɗa harkokin kasuwanci da ilimi musamman ilimin ‘ya’yansu.

Haka kuma Kwamishiniyar ta ƙara da kira ga matan ‘yan kasuwa da su tabbatar da sun nemi ilimin harkokin kasuwanci kamar yadda Musulunci ya tanada.

Shi ma Kwamishinan matasa da wasannin na Jihar Kebbi Alhaji Nura Fingilla ya yi godiya ta musamman ga uwargidan Gwamnan Kebbi wajen irin gudunmawar da take bai wa matasa ta ɓangaren sana’o’in dogaro da kai musamman koyon sana’o’i daban-daban.

Ita ma sakatariyar dindindin ta hukumar kasafi da tsare-tsaren tattalin arzikin jihar Kebbi Hajiya Aisha Usman da take jawabi a wurin taron, ta yi kira ga mata ‘yan kasuwar da su sanya juriya da himma a harkokin kasuwancinsu.

Haka kuma wakilan hukumar SMEDAN da NAFDAC  sun gudanar da jawabai a wurin taron inda suka bayyana cewa yana da kyau su hada hannu da SMEDAN don samun karin ilmin hanyaoyin gudanar da kasuwanci a matakai dabam-daban musamman matakin farko.

By Editor