Naira 100,000 ba zai riƙe rayuwar ma’aikaci ba – Majalisar Wakilai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Majalisar Wakilai ta bayyana cewa ya zama wajibi a daidaita albashin ma’aikatan Nijeriya, domin kuwa ƙasa da Naira 100,000 a wata ba zai riƙe rayuwar ma’aikaci ba.

Majalisar ta ce ɗauki matakin tabbatar da ƙarin albashi ga ma’aikatan Nijeriya.

An cimma wannan matsaya ne a zaman da aka yi a ranar Laraba, biyo bayan ƙudirin da shugaban marasa rinjaye Kingsley Chinda da wasu 39 suka gabatar.

Yayin muhawara kan ƙudirin mai taken “Buƙatar ƙarin albashin ma’aikata a Nijeriya,” mataimakin shugaban marasa rinjaye Aliyu Madaki ya bayyana ƙalubalen da ‘yan Nijeriya ke fuskanta sakamakon hauhawar farashin kayayyaki.

Ya jaddada muhimmancin samun albashi mai tsoka da adalci ga ma’aikata, kamar yadda aka zayyana a cikin doka ta 23 ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta kare haƙƙin ɗan Adam.

Madaki ya kuma yi nuni da ƙudurin ‘
Nijeriya na samun cigaba mai ɗorewa, wanda ya buƙaci a biya ma’aikata albashi mai tsoka.

Ya ƙara da cewa, janye tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi a baya-bayan nan ya sa aka ƙara farashin sufuri da kuma kayan abinci, wanda hakan ya sanya aka sanya sabon albashin ma’aikata.

Yayin da yake amincewa da karin mafi ƙarancin albashi da shugaban ƙasa ya yi a baya-bayan nan, Madaki ya jadadda cewa ƙarfin sayen ma’aikata ya ragu saboda tsadar rayuwa da kuma faɗuwar darajar Naira.

Dangane da waɗannan ƙalubale, majalisar ta bayyana cewa babu wani ma’aikaci da zai iya rayuwa da albashin ƙasa da N100,000.00 duk wata a Nijeriya.

Madaki ya yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki matakin gaggawa na inganta matakan samun kuɗin shiga ba, ’yan Nijeriya da dama za su faɗa cikin talauci, wanda hakan zai haifar da fatara da kuma rasa kimar gwamnati.

Dangane da ƙudirin, mataimakin shugaban majalisar Benjamin Kalu ya kafa kwamitin wucin gadi domin tantance hanyoyin aiwatar da albashin ma’aikatan Nijeriya.

Majalisar ta kuma umurci kwamitocinta na kuɗi da tsare-tsare da ci gaban tattalin arziki da su sake duba ƙudirin su miƙa ƙudurin ga Majalisar Dattawa domin amincewa.