La Liga za ta binciki batun cin zarafin Vinicius

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

La Liga na nazarin wani bidiyo da ake zargin yana nuna wariyar launin fata ga Vinicius Jr a wasan da Real Madrid ta buga da Valencia a ƙarshen makon da ya gabata.

Bidiyon da aka wallafa a shafukan sada zumunta na Intanet ya nuna yadda wani yaro mai goyon bayan Valencia ke jagorantar cin zarafin ɗan wasan.

Vinicius ya zura ƙwallaye biyu a wasan da suka tashi 2-2 a ranar Asabar kuma ya yi murna ta hanyar ɗaga hannunsa sama.

Ɗan wasan mai shekaru 23 ya fuskanci cin zarafi na wariyar launin fata sau da dama a wasanni daban-daban a Sifaniya.

A cikin Mayu 2023, Vinicius ya ce “La Liga ta masu wariyar launin fata ce” bayan da magoya bayan Valencia suka muzanta shi a filin wasan Mestalla.

Daga baya an kama wasu mutane uku da laifin cin zarafi sannan aka ci tarar Valencia tare da rufe wani vangare na filin wasanta na wasanni biyar, wanda daga baya aka rage zuwa wasanni uku bayan ƙungiyar ta ɗaukaka ƙara.