El-mustapha ya nuna alhini kan rasuwar mahaifiyar Afakallah

Daga BASHIR ISAH

Sakataren Hukumar Tace Finafinai na Jihar Kano, Alh. Abba El-mustapha, ya nuna alhininsa kan rasuwar mahaifiyar tsohon sakataren hukumar, Malam Na’abba Afakallah.

Sanarwar da hukumar ta fitar ranar Juma’a ta bakin Jami’in Yaɗa Labarai, Abdullahi Sani Sulaiman, ta ce Hajiya Gwaggo ta rasu ne bayan fama da rashin lafiya.

Abba El-mustapha ya bayyana marigayiyar a matsayin uwa tagari, kuma abar koyi wadda rasuwarta ta haifar da wagegen giɓi a cikin al’umma.

Ya ƙara da cewa, mutuwarta babban rashi ne ba ga ahalinta kaɗai ba har ma da al’ummar Musulmi baki ɗaya.

Daga nan, El-Mustapha ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayiyar kura-kutanta, Ya kuma sanya ta cikin Aljanna firdausi.