Canjin Dala kashi biyar ne a Nijeriya – Bashir Na’iya

Daga AMINA YUSUF ALI

Duk da cewa ‘yan kasuwa su ma suna da rawar da za su taka wajen samun sauƙin tsadar kaya, amma ka da mu yi ta jibga musu laifi ba tare da mun dubi yadda canjin dalar kanta ya koma ba a Nijeriya. A halin da ake ciki yanzu a Nijeriya canjin dollar ya kasu kusan kashi biyar, kowa yana da farashinsa na canji. Misali:

Canjin CBN daban,
Canjin bayan fage ko kamfanonin canji daban,
Canjin hukumar kwastam daban,
Canjin ‘yan Fesbuk ma daban,
Canjin mazauna ƙasashen waje daban.

Wallahi ni wannan bambanci har dariya yake ba ni, na rasa sanin me ya haifar da shi? Babban abun mamakin ma shi ne, mu da muke wajen Nijeriya muna manhajoji na hada-hadar kuɗaɗe da yawan gaske, kusan kullum sai na ga tallan manhajoji na hada-hadar kuɗaɗe wanda ban tava gani ba a baya, misali irin su Nairaland, Nala, Afriex, taptap, ga su nan dai barkatai.

Amman babban abun mamakin da na kasa ganewa shi ne, me ya sa su waɗannan manhajoji na hada-hadar kuɗaɗe farashinsu har ya fi na CBN? Kuma fa kai tsaye suke harka da shi CBN ɗin.

An ce canjin dala a CBN tsakanin ₦1,300 zuwa ₦1,400 ne, amma su kuma wadannan manhajoji suna ba mu canji har kusan ₦1,600 kuma da CBN suke harkokinsu, to me ya sa canjinsu ya fi na CBN? Waye yake cika musu, ta yaya suke samun riba? Ku fahimce ni da kyau su fa a hukumance suke hada-hadarsu kai tsaye da CBN, kuma daga CBN suke karvar duk wani bayani, domin su suka aiko min da imel a baya cewar CBN sun soke bayar da daloli sai dai Naira. Kai wata manhajar ma har ladan gabe suke bayarwa, to ya abun yake ne?

Ina fatan masana ko duk wanda ke da masaniya zai yimin bayanin yadda abun yake.

Bashir Ibrahim Na’iya, mazaunin Ma Maryland ta ƙasar Amurka, masanin tattalin arziki ne kuma ɗan kasuwa, sannan mai yin sharhi ne a kan lamurran yau da kullum.