Gwamnatin Tarayya za ta yaƙi miyagun ɗabi’u tsakanin ɗaliban sakandare

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi

Gwamnatin Tarayya ta yi kira akan haɗin kai wajen yaƙi da miyagun ɗabi’u a makarantun sakandare a faɗin Nijeriya.

Maigirma Ministan Ilmi na Ƙasa Honarabul Yusuf Tanko Sununu ne ya yi wannan kiran yayin wata ganawa da wani sashen malamai, ɗalibai da iyayen yara a lokacin wata faɗakarwa akan hanyoyin da za a bi wajen magance matsalolin miyagun ɗabi’u a makarantun sakandare a faɗin Nijeriya.

Ministan ya bayyana cewa waɗansu daga cikin hanyoyin da za su magance matsalolin miyagun ɗabi’u tsakanin yara ɗaliban sakandare sun haɗa da sake farfaɗo da ƙungiyoyin makarantun sakandare irin na da wato School Clubs and Societies waɗanda suke da manufofin samar da kyawawan ɗabi’u a tsakanin yara matasa ‘yan makaranta da suka haɗa Red Cross, Boy Scout of Nigeria, Press Club da dai sauransu.

Haka kuma ministan ya yi amfani da wannan damar wajen janyo hankalin ɗalibai akan illar miyagun ɗabi’u inda ya yi kira a gare su da cewa yanzu ne ya kamata su tsaya su nemi ilimi domin gobensu da kuma kyawawan ɗabi’u su kuma guji munanan ɗabi’u musamman a wannan zamani da muke ciki na kafafen sada zumunta.