Hukumar Kwastom za ta binciki sanadin turmutsitsi a wurin cinikin shinkafa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Hana Fasa-ƙwauri ta Nijeriya, NCS, ta kafa kwamitin da zai binciki al’amuran da suka janyo turmutsitsin da kuma asarar rayuka da aka samu a tsohon ofishinta da ke Yaba, Legas.

Shugaban hukumar Bashir Adeniyi, ya umurci kwamitin ƙarƙashin jagorancin wani jami’in hukumar da ya zaƙulo waɗanda rikicin ya rutsa da su tare da tsara hanyoyin bada tallafi ga iyalansu.

Haka zalika, shugaban ya dakatar da rabon ne domin jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu yayin da hukumar da ƙoƙarin samar da dabarun yadda za a cigaba da rabon cikin kwanciyar hankali.

Bugu da ƙari, jami’in hulɗa da jama’a na hukumar ta ƙasa, Abdullahi Maiwada a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja, ya ce hukumar za ta yi bincike sosai kan wannan turmutsitsin tare da gyara kura-kurai da dama.