Ramadan: Abincin da ya kamata a ci da waɗanda za a ƙaurace wa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Miliyoyin Musulmai a faɗin duniya sun fara azumin watan Ramadana, ɗaya daga cikin watanni masu tsarki a addinin Musulunci.

A lokacin Sahur (kafin alfijir) da kuma buɗa baki (magariba), yana da kyau a san takamaiman nau’ikan abincin da ya kamata a ci don tabbatar da ɗorewar kuzari da jin daɗin rayuwa gabaɗaya.

Abubuwan da ya kamata a ci lokacin Sahur:

A yayin Ramadan idan kana son ka yini da kwarinka da lafiya shi ne a ci abinci mai gina jiki, da sauransu, kuma dole ka sha ruwa sosai.

A kuma ci abinci mara nauyi mai lafiya yayin shan ruwa.

Yana da kyau a ci abinci mai nauyi lokacin sahur, ko kuma nau’ukan abincin da suke tsaba, saboda da a hankali suke narkewa, za su riƙa bai wa mutum kwarin jiki a duka yinin.

Kamar haka dai tsaba burodi da sauran abubuwa yayin sahur.

Bincike ya nuna cewa na’in abinci irin su wake da sauransu za su iya ƙarawa mutum ƙwarin gwiwa da kashi 30.

Yana da kyau a sha ruwa isasshe sai ka ga a duka yinin ba ka ji ƙishi ba. Sannan kuma a kiyayi sahur da abubuwa masu gishiri.

Abinci mai gishiri yana sa ƙishi, kuma kamata ya yi ya zama abu na ƙarshe da mutum zai ci. Doguwar rana ce da za ka daɗe kana jin ƙishi a cikinta.

Abubuwan sa ya kamata a ci lokacin buɗa baki:

Abu ne sananne lokacin shan ruwa an fi so a yi buɗa baki da dabino kamar yadda yake a addinance, sannan a bi shi da abubuwa masu ruwa da sikari, kuma wannan ce hanyar da Fiyayyen Halitta ke shan ruwa da ita.

Hanya ce mai kyau buɗe baki da dabino da kuma ruwa, sannan su buɗe maka hanyar cin abinci. Za su ƙara maka kwarin jiki su hana ka jin ƙishi.

Bayan kwashe yini ba tare da cin komi ba, bai kamata mutum ya yi buɗa baki ba da abu mai nauyi, nan da nan za su sanya ka ji ka gaji, ka ji kasala da kuma rashin lafiya a wasu lokutan.

Abin da ake ci bayan wannan ya sha banban da al’ada da kuma al’umma, ko wa da irin abin da yake ci a nahiyarsa, amma kan wannan ba wata ƙa’ida.

Wasu ƙwararru kan abinci na bayar da shawara kan cewa ka da a ci abincin buxa baki da yawa lokaci guda, kamata yayi a raba shi gida biyu, wannan zai taimaka wajen narkewar abincin da aka ci cikin gaggawa.

Yana da kyau a ƙauracewa shan lemun kwalba da kuma abubuwa masu ɗan karam zaƙi.

A ƙaurace wa cin soyayyun abubuwa, domin su na hana narkewar abinci da wuri.