Zargin cushe a kasafin 2024: Yadda dakatar da Sanata Ningi ta tada ƙura a Nijeriya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A Nijeriya, jam’iyyun hamayyar ƙasar sun yi Allah-wadarai da matakin da majalisar dattawa ta ɗauka na dakatar da Sanata Abdul Ningi na tsawon wata uku, bayan da ya yi wasu kalamai da ke nuna an cusa wasu kuɗi naira kusan tiriliyan huɗu, waɗanda ba a san inda aka nufa da su a kasafin kuɗin ƙasar na bana ba.

Jam’iyyun hamayyar suna ganin kamata ya yi a fara da gudanar da bincike kan batun cushen kuɗin, don a tabbatar da gaskiya ko akasin zargin, kafin a ɗauki matakin dakatar da ɗan majalisar.

Matakin dakatar da Sanata Abdul Ningi, na tsawon wata uku da majalisar dattawan Nijeriyar ta ɗauka, na ci gaba da shan suka, har ma bakin wasu jam’iyyun hamayya na ƙasar ya zo ɗaya, wajen yin tir da lamarin.

Jam’iyyarsa ta PDP, ta bayyana matakin a matsayin wani yunƙuri na hana gudanar da bincike, da yin balulluba, da kuma yi wa ‘yan Nijeriya wuji-wuji ina gabas kan batun da ya bankaɗo.

Jam’iyyar ta ce tana goyon bayan Sanatan nata game da matakin da ya ɗauka na yayata badaƙalar da yake zargin an yi, a cewar Ibrahim Abdullahi, muƙaddashin jami’in hulɗa da jama’a na ƙasa na jam’iyyar.

“Ya yi abin da ya dace wanda muke goyon baya a matsayinmu na jam’iyya, kuma na tabbata duk ‘yan Nijeriya na goyon bayan wannan ƙorafi da aka yi saboda irin wannan zaluncin ne ya durƙusar da Nijeriya,” in ji Ibrahim Abdullahi.

A nata ɓangaren, jam’iyyar PRP, na ganin akwai lauje cikin naɗi, game da matakin dakatar da ɗan majalisar dattawan.

Abdullahi Ahmad Wakili, wani tsohon ɗan takarar kujerar sanata na jam’iyyar a jihar Kaduna, ya ce, “maimakon majalisar ta kafa kwamitin bincike domin gano gaskiyar lamarin, sai kawai aka dakatar da shi na wata uku, saboda haka mu a matsayin jam’iyarmu ba mu yarda da hakan ba, kuma muna kira ga duk hukumomin bincike da su gudanar da bincike.”

Jam’iyar LP ita ma ta nuna damuwarta kan matakin, inda kakakin jam’iyyar, Dakta Yunusa Salisu Tanko, ya ce suna tare da bayanin da Sanata Ningi ya yi kuma suna kira da a yi bincike kan bataun kasafin kuɗin.

Lamarin dai na ci gaba da ɗaukar hankali tare da haifar da ce-ce-ku-ce a Nijeriya, kuma ana nan an zura ido a ga yadda a ƙarshen lamarin zai kaya.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne ya bayyana sanarwar dakatar da Ningi, bayan dakatarwar ta samu goyon bayan mafiya yawan mambobin Majalisar Dattawa ɗin, a zaman da Majalisar ta yi matsayin kwamitin su baki ɗaya.

“Ina sanar da dakatar da Ningi tsawon watanni uku daga duk wasu aikace-aikace da suka shafi Majalisar Dattawan Nijeriya,” inji Akpabio.

Dakatarwar dai ta biyo bayan ƙorafin da Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Kuɗaɗe, Sanata Adeola Olamilekan.

Ningi wanda shi ne Shugaban Ƙungiyar Sanatocin Arewa (NSF), kwanan nan ne ya shaida wa BBC Hausa cewa ‘yan majalisa sun kira mai bin diddigin kuɗaɗe mai zaman kan sa, wanda ya bankaɗo yadda aka yi cushen Naira tiriliyan 3 cikin Kasafin 2024.

“Misali, muna da kasafi na Naira tiriliyan 28, amma bayan an yi bincike da bin diddigi, an gano cewa tantagaryar kasafin kuɗin Naira tiriliyan 25, sauran tiriliyan 3 kuma cushe ne aka yi. To me za a yi da Naira tirliyan ukun da aka cusa a kai?”

Idan ba a manta ba, su ma sanatocin Arewa sun tunkari Akpabio, inda suka zarge shi da cusa Naira tiriliyan 4 a cikin kasafin 2024.

Idan za a tuna, a ranar Litinin Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata zargin da Sanata Ningi ya yi, inda ta kira shi tantirin maƙaryaci.

CISLAC ta gargaɗi Majalisar Dattawa kan yin shiru a kan ra’ayoyin ‘yan adawa Ƙungiyar Civil Society Legislative Advocacy Centre, CISLAC/Transparency International a Nijeriya, TI-Nigeria, ta gargaɗi majalisar dattawan Nijeriya game da yin shuru ba bisa ƙa’ida ba ga ‘yan majalisun jam’iyyar adawa.

Babban Darakta na CISLAC, Auwal Musa-Rafsanjani, wanda ya yi gargaɗin a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, ya bayyana damuwarsa kan hare-haren da ake kaiwa ‘yancin faɗin albarkacin baki, ‘yancin ‘yan adawa da ‘yancin cin gashin kansu a zauren majalisar dokoki.

Mista Rafsanjani yana mayar da martani ne kan dakatarwar da Majalisar Dattawa ta yi wa Sanata Abdul Ningi kan fallasa Naira tiriliyan 3 da Majalisar ta yi wa kasafin kuɗin 2024 a bainar jama’a.

A cewar shugaban hukumar CISLAC, an fara dakatar da Sanata Ningi ne saboda ya bayyana damuwarsa da yadda tsarin mulki ya amince da shi kan kasafin kuɗin shekarar 2024 ‘a wannan mawuyacin lokaci da al’ummar ƙasar ke cikin mawuyacin hali a cikin matsalar tattalin arziki.

“Dakatar ba ta rasa nasaba da fallasa Naira tiriliyan 3 da Majalisar Dattawa ta yi wa kasafin kuɗin shekarar 2024, wanda har ya zuwa yanzu ta kasa nuna gaskiya da riƙon amana a cikin kasafin kuɗin.

“Wannan ya haɗa da rashin daidaito da rashin gaskiya da amana da ke tattare da rabon Naira tiriliyan 3, inda ake sa ran kowane Sanata zai karɓi Naira miliyan 500 a matsayin alawus-alawus na mazavu.

“Mun gane kuma mun tabbatar da cewa ‘yancin faɗin albarkacin baki da ra’ayi sun kasance masu tsattsauran ra’ayi don kiyaye dimokuraɗiyya, ɗabi’u da ƙa’idoji a Nijeriya.

“Mu ba tare da vata lokaci ba, mun tabbatar da matsayinmu na cewa ‘yancin faɗin albarkacin baki da kuma ‘yancin faɗi wani haƙƙi ne da tsarin mulki ya ba shi kuma haƙƙi ne da doka ta amince da shi a ƙarƙashin sashe na 39 na kundin tsarin mulkin Tarayyar Nijeriya na 1999; Mataki na 19 na Yarjejeniyar Haƙƙin Ɗan Adam ta Duniya, 1948; Mataki na 19 (2) na Yarjejeniya Ta Duniya Kan ‘Yancin Bil’adama da Siyasa, 1966; don haka dole ne a kiyaye tsafta da tsarkin waɗannan tanade-tanade, nunawa da kuma kare su daga wata cibiya ta jama’a irin ta majalisar ƙasa.

“Duk wani abu da ke cikin waɗannan tanade-tanaden, yana daidai da take haƙƙin ɗan Adam da gangan da kuma rashin mutunta doka.

“Dole ne mu sake jaddada cewa Kundin Tsarin Mulki na 1999 na Tarayyar Nijeriya a matsayin babbar doka ta ƙasa ya ba Majalisar Dattawa tazarar ikon dakatar da ɗan Majalisar Tarayya.

“Irin waɗannan tanade-tanaden ana samunsu ne kawai a cikin dokokin kwamitin da’a da gata, wanda ke amsa taron ta hannun shugaban majalisar dattawa. A kan wannan bayanin, dokokin Kwamitin ba za su iya ƙetare Kundin Tsarin Mulki ba, musamman ma game da ‘yancin faɗar albarkacin baki wanda yake haƙƙi ne na asali.

“Kamar yadda kowane ɗan majalisar tarayya mai wakiltan mazaɓarsa ke da hurumi na farko da ya rataya a wuyan jama’a da kuma bayar da ra’ayi ga jama’a domin a yi musu hisabi, haka nan bai kamata a tsoma baki ko a tsoratar da su ko kuma a danne su ba,” cibiyar ta jaddada.

Mista Rafsanjani ya bayyana fargabarsa cewa matakin danniya da shugabancin majalisar dattijai zai ɗauka a fili ƙarara ya nuna ɓangaren majalisar a matsayin mai mulkin kama karya, wanda kuma zai yi mummunar tasiri ga ‘yancin ‘yan majalisar, da muhawara mai ƙarfi, da gabatar da gaskiya, da kuma martabar majalisar a gaban ‘yan Nijeriya.

Ya ce: “Dakatar da Sanatan da ke wakiltar mazaɓar majalisar dattijai baki ɗaya ba bisa ƙa’ida ba daidai yake da nuna al’adar yin shiru da rashin hankali da rashin mutunta jama’a.”

“Duk da yawan jam’iyyun adawa a Majalisar Dokoki ta Ƙasa, ga dukkan alamu an ci su da ƙarfin ikon ɓangaren zartarwa da kuma manyan jami’an majalisar.

“Saboda haka, muna kira ga majalisar dattawa da ta gaggauta yin watsi da ra’ayoyin ‘yan adawa a majalisar; kamar yadda jigon majalisa shi ne ba da damar ‘yancin faɗin albarkacin baki da saɓanin ra’ayi tare da samar da tsarin dimokuraɗiyya na muhawara mai ma’ana da ke bunƙasa muradun ɗasa.

“Babban hatsarin shi ne, ba za a iya barin ‘yan majalisa su yi aikinsu ba da suka haɗa da sa ido da kuma ra’ayoyi na adawa da ɓangaren zartarwa da manyan jami’an majalisar dattijai wanda zai kai ga kama-karya ta dimokuraɗiyya.

“Muna kira ga dukkan ‘yan Nijeriya masu kishin ƙasa da kafafen yaɗa labarai da su kare tare da yin watsi da duk wani mataki ko matakin da Majalisar Dokoki ta ƙasa ta ɗauka na rashin bin tafarkin dimokuraɗiyya da aka yi niyya don kawo cikas ga al’amuran jama’a da kuma durƙushewar al’umma,” in ji sanarwar.

By Editor