Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Shugaban Asibitin PHC Kabuga, Yusuf Adamu Muhammad Kabuga a Ƙaramar Hukumar Gwale ya bayyan cewa karrama shi da lambar yabo abin farin ciki ne gare shi da ma’aikatan asibitin Kabuga PHC, da sashin lafiya na ƙaramar hukumar Gwale da ma’aikatar lafiya da sauran masu ruwa da tsaki na Kano kamar yadda Kwamared Yusuf Adamu Muhammad ya bayyana a lokacin da ya karɓi kyautar karramawa ga ƙungiyar Health Awareness a makon da ya gabata.
Haka kuma Malam Yusuf ya ce aikin lafiya aiki ne na jama’a da ke buƙatar kulawa da nutsuwa, da haƙuri da jajircewa, “don haka za mu ci gaba da jajircewa fiye da yadda ake tunani domin hakan shi ne zai kawo ci gaban kiwon lafiya da walwalar jama’a kamar yadda ya kamata musamman ƙaramar hukuma ta Gwale yadda ta ke da masu tarin ilimin addini da na zamani a ce an ba ka wannan lamba kan ƙoƙarin aiki wannan abun a gode wa Allah da wannan ni’ima ne.”
A ƙarshe Kwamred Yusuf wanda shi ne shugaban ƙungiyar ma’aikatan lafiya na ƙaramar hukumar Gwale ya ce asibitin Kabuga da ɗaukicin ma’aikatansa za su ci gaba da ƙoƙari da tausayi da nuna tarbiyya ga marasa lafiya da shugabaninsu na ƙaramar hukuma da na jihar Kano baki ɗaya.
