Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi
Gwamnan Jihar Kebbi Malam Nasir Idris ya jinjina wa jami’an kashe gobara na tarayya da ke aiki a jihar Kebbi bisa ga gamsuwarsa ga irin ƙoƙarin da su ke yi wajen ceto rayuwa da dukiyoyin al’umma a duk lokacin da wani iftila’in wuta ya tashi a wani waje.
Ya bayyana haka ne a garin Birnin Kebbi yayin da yake ƙaddamar da sabuwar motar kashe gobara ta zamani ga jami’an a gidan gwamnatin jihar Kebbi.
Ya bayyana cewa yana da kyau su haɗa hannu da takwaransu na jiha don samun nasarori wajen aiwatar da ayyukansu a cikin jiha.
Haka-zalika maigirma Gwamna ya umarci Sakataren Gwamnatin jiha Alh.Yakubu Bala Tafida da ya zauna da waɗannan jami’an domin taimaka musu akan abubuwan da suke buƙata wajen tafiyar da ayyukansu na taimakon al’umma musamman dangane da abinda ya shafi samar da man fetur da samar da wadataccen ruwa da sinadaran da ake amfani da su wajen kashe wuta.
Ya bayyana cewa wannan aikin ba wani mutum ko wata hukuma da ke iya biyansu sai dai Allah ya saka musu da alheri.
Ya kuma yi kira ga al’umma musamman mata masu amfani da iskar gas wajen dafa abinci da su su rinƙa kulawa da kyau don tabbatarda sun kashe gas bayan kammala aikin girki don kaucewa afkuwar iftila’in gobara.
