Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Yayin da a yankuna da dama na Arewa maso Yamma ake fama da mummunan rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma, a Jihar Jigawa kuwa Gwamnan Jihar Jigawa Umar Namadi ya bayyana yadda ya sasanta tsakanin manoma da makiyaya da ke rikici a Ƙaramar Hukumar Guri da ke Jihar Jigawa.
Cikin bayanan sa kamar yadda Ofishin Sabbin Kafafen Yaɗa Labarai na Zamani, wato New Media Office ya bayyana, Gwamna Namadi ya ce, an sanar da shi yadda wani shugaban Fulani ya zama ƙadangaren bakin tulun da ke ke da hannu dumu-dumu wajen rura wutar rikici tsakanin ɓangarorin biyu, wadda har ya yi barazanar ɗaukan tsattsauran mataki akan sa.
“Gwamna Namadi ya ce, ɗaukar tsauraran matakai akan lamarin abu ne da ya zama wajibi domin ceto rayukan dubban mazauna yankin waɗanda rikicin yankin ya ke rutsawa da su.
“Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya halarci wani gagarumin biki da aka gudanar a ranar Lahadi a rigar Boɗala a Ƙaramar Hukumar Guri, domin murnar wanzuwar zaman lafiya a yankin.
“Na gayyace shi mun zauna da shi (Lamiɗo Giɗe) kuma a gaban Kwamishinan ‘Yan Sanda na faɗa masa cewa, dole ne ɗaya daga cikin biyu ya faru, ko dai ka bar zaman lafiya ya wanzu a wannan yanki, ko kuma in ba da umarnin harbe ka. A shirye na ke da na yi duk wata mai yuwuwa don ceto dubban rayukan alumma,” a cewar Gwamna Namadi.”
Ofishin New Media ɗin ya wallafa cewa “Gwamnan wanda yake jawabi cike da annuri, ya ce an samu sulhu a tsakanin ɓangarorin biyu bayan ƙulla yarjejeniya da Lamiɗo Giɗe wanda da farko ya ke da kuskuren fahimtar zaman lafiya tsakanin al’umma.”
“Ba za a iya ƙididdige rawar da Lamiɗo Giɗe ya taka wajen wanzar da shirin wannan zaman lafiya ba. Yin adalci ga kowane ɓangare shi ne zai tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin ɓangarorin da ke rikici da juna. “Da na amince da batun da aka yi a baya game da Lamiɗo Gide na cewa ba zai taɓa barin zaman lafiya ya wanzu a wannan yanki ba, ba tare da na gayyace shi ba, da mun shiga cikin matsala har ya zuwa yanzu,” in ji gwamnan a wajen taron wanda shi ma Lamiɗo Gide ya halarta.”
A wurin taron, Namadi ya ja hankalin makiyayan ‘yan asalin yankin da su sa ido game da karɓar baƙin mutane da ke shigowa su cakuɗu da su.
“Kada ku zura ido baƙin mutane su zo su ɓata zaman lafiya da muke da shi na tsawon shekaru.
“Kada wanda ya bari wani baƙuwar fuska ya zauna ba tare da izinin Sarkin Hadejia ba,” in ji gwamna Namadi.
Ƙaramar Hukumar Guri da yankin ƙaramar Hukumar Kirikasamma da ke makwabtaka da juna, yanki ne da ke da ƙasa mai albarkar noma da kiwo. Sai dai fafutikar neman mallakar wuraren dausayi ya haifar da munanan rigingimu tsakanin manoma da makiyaya shekara da shekaru, kamar yadda ofishin ya ruwaito.
Baya ga kiwo da noma, dajin na da halittu kusan nau’in tsuntsaye masu ƙaura aƙalla 378 daga yankunan Turai da Austaraliya.
Wasu mazauna yankin sun ce jami’an Gidauniyar Kare Namun Dajida suka haɗa da Yarima Philip da Sarki Charles sun ziyarci yankin.
Duk da cewa a tsawon shekarun da suka gabata yankunan biyu sun sha fama da rikicin manoma da makiyaya, amma ƙaurar da makiyayan ke yi a yankin ya ƙara ta’azzara rikicin, wanda ya yi sanadiyyar laƙume rayukan mutane da dama.
