Ƙarancin abinci: CBN ya bada tallafin taki buhu miliyan 2.15 domin raba wa manoma a Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ma’aikatar noma da wadatuwar abinci ta karɓi buhunan takin zamani guda miliyan 2.15 daga Babban Bankin Nijeriya, CBN.

Za a raba takin ne ga manoma domin daƙile hauhawar farashin kayayyakin abinci a ƙasar tare da bunƙasa samar da abinci da kuma wadatarsa.

Abubakar Kyari, ministan noma da wadatuwar abinci wanda ya yi jawabi a wajen taro a ranar Laraba a Abuja, ya nuna godiya ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da CBN bisa wannan karimcin.

Kyari ya tabbatar wa Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, cewa za a yi amfani da kayan cikin adalci tare da kai wa manoman da ke da buƙata.

Tun da fari Cordoso ya bayyana farin cikin da zaiyarar da kuma miƙa takin ga ma’aikatar noma, wanda a cewarsa zai yi maganin hauhawar farashin abinci.

A cewarsa, farashin kayan abinci na daga cikin muhimman abubuwan da ke tattare da hauhawar farashin kayayyaki.

Ya ce babban bankin na CBN na da burin inganta haɗin gwiwarsa da ma’aikatar domin inganta samar da abinci.