Daga AISHA ASAS
Daya daga cikin matsalolin da likitoci suka ce sun fi yawaita a matsalar ƙafa ita ce warin kafa. Masana sun bayyana cewa, warin ƙafa ba wai zufa kadai ke haddasawa ba, illa haɗuwar zufa da ƙwayoyin cuta da ke rayuwa a fata ko cikin takalma.
A cewar masana, idan mutum ya saba sanya takalma rufaffe na tsawon lokaci ba tare da barin ƙafa ta sha iska ba, hakan na ƙara haddasa warin kafa.
Likitan fata Dakta Hafsat Bello ta ce: “Warin ƙafa na iya shafar kuzarin mutum da mu’amalarsa da jama’a. Amma abu ne da za a iya magancewa idan aka bi tsafta da kulawar da ta dace.”
Masana sun ce daga cikin hanyoyin rage warin ƙafa akwai gujewa sanya takalma guda ɗaya kullum ba tare da sun samu damar bushewa ba. Sun kuma bayyana cewa, barin takalma su sha iska bayan amfani na rage taruwar ƙwayoyin cuta da danshi. Haka kuma amfani da powder ko spray masu rage zufa da danshi na taimakawa wajen daƙile warin ƙafa, yayin da wanke ƙafa bayan doguwar tafiya ko aiki ke taimaka wa wajen kare fata daga kwayoyin cuta.
