Daga AISHA ASAS
Mai karatu, sannunku da jimirin bibiyar shafin Iyali na jaridar Blueprint Manhaja.
A shekarun baya, an daɗe ana kallon mace a matsayin mai kula da gida kawai, wadda aikinta ya taƙaita ga girki, rainon yara da kula da miji. Sai dai sauyin zamani, hauhawar farashin kayayyaki da matsin tattalin arziki sun sauya wannan fahimta a hankali, har ta kai ga yau dubban mata ke rungumar sana’o’i daban-daban domin tallafa wa kansu, iyalansu da ma al’ummar da suke rayuwa a cikinta.
Ba wai neman abin duniya kawai ne ya jawo wannan sauyi ba. A’a, mata da dama sun fahimci cewa sana’a na daga cikin hanyoyin da ke tabbatar da kwanciyar hankali, rage tsananin buƙata da kuma ba iyali damar fuskantar ƙalubalen rayuwa cikin mutunci.
A zahiri ma, idan aka waiwayi gidaje da dama, za a tarar da sana’ar uwa ta zama ginshiƙin da ya hana iyali durƙushewa. Akwai yaran da suka ci gaba da karatu saboda gudunmawar da uwa ke bayarwa wajen biyan kuɗin makaranta. Akwai gidajen da suka kuɓuta daga tarin bashi ko kunyatar rayuwa saboda mace ta rungumi sana’a ta halal ta zama abin dogaro a lokacin tsanani.
Masu nazarin tattalin arziki da zamantakewar al’umma sun daɗe suna bayyana cewa, bai wa mace damar samun halal yana amfanar iyali ne baki ɗaya. A mafi yawan lokuta, abin da mace ta samu kan koma ne wajen kula da gida, tarbiyyar yara da kuma inganta rayuwar iyalanta.
Sai dai duk da wannan ci gaba, har yanzu ana samun wasu da ke kallon sana’ar mata da idon son rai ko tsohuwar fahimta. Wasu na ganin cewa da zarar mace ta fara samun kuɗin kanta, za ta raina mijinta ko ta daina mutunta shi. Amma abin tambaya shi ne, shin kuɗi ne ke rusa tarbiyya, ko kuwa rashin tarbiyya tun asali?
Abin da ake gani a zahiri shi ne mace mai nagarta ba ta amfani da sana’arta wajen tayar da fitina ko rusa zaman lafiya. Akasin haka ma, tana kallon abin da take samu a matsayin wata hanya ta rage wa mijinta nauyi, ta taimaka wa ‘ya’yanta da kuma tabbatar da zaman lafiya a gidanta.
A ɓangaren addini kuwa, babu shakka Musulunci bai hana mace neman halalinta ta fuskar sana’a ba matuƙar tana kiyaye mutuncinta da dokokin addininta. Tarihi ya nuna cewa, Khadija bint Khuwaylid, Allah Ya ƙara yarda a gare ta, ta kasance fitacciyar ‘yar kasuwa tun kafin aurenta da Annabi Muhammad (SAW), kuma hakan bai rage mata daraja ko matsayinta ba.
Abin da addini ya fi mayar da hankali a kai shi ne halalcin abin da ake yi, gaskiya cikin mu’amala da kuma tsoron Allah. Idan waɗannan suka tabbata, sana’a ta zama wata ƙofa ta neman arziki mai albarka.
Wani babban ƙalubalen da ke hana wasu mata shiga sana’a shi ne tsoron fara sana’a da ƙaramin jari. Alhali tarihi ya nuna cewa, manyan kasuwanci da dama sun fara ne daga ƙanana. Ba girman jari ne kaɗai ke haifar da nasara ba, sau da yawa jajircewa, haƙuri da kyakkyawan tsari su ne tubalin da ke gina babban rabo.
A Najeriya ma akwai mata masu yawa da suka fara da ƙananan sana’o’i kamar ɗinki, girke-girke, sayar da kayan miya ko abubuwan sha, amma daga baya suka bunƙasa har suka mallaki manyan kasuwanci tare da samar wa wasu aikin yi. Wannan darasi ne mai nuna cewa sana’a ba hanyar neman kuɗi kawai ba ce, hanya ce ta gina kai, gina iyali da kuma ba da gudunmawa ga ci gaban al’umma.
Sai dai kamar yadda ake buƙatar mace ta bunƙasa kanta, haka kuma akwai buƙatar kada neman abin duniya ya shagaltar da ita daga nauyin tarbiyyar gida. Hikima ita ce a samu daidaito tsakanin neman halal da kula da amanar da Allah Ya ɗora wa kowane ɓangare na iyali.
Haka nan akwai buƙatar mazaje su zama masu ƙarfafa gwiwar matansu maimakon zama masu hana su duk wata hanya ta neman halal. Gidajen da ke ginuwa a kan fahimtar juna, haɗin kai da taimakon juna su ne suka fi samun kwanciyar hankali da ɗorewar zaman lafiya.
Iyaye ma na da muhimmiyar rawa wajen koya wa ‘ya’yansu mata sana’a tun suna ƙanana. Irin wannan tarbiyya na haifar da jajircewa, dogaro da kai da kuma rage yiwuwar faɗawa cikin wasu matsalolin rayuwa da zaman banza kan haddasa.
Akwai buƙatar gwamnati, masu hannu da shuni da ƙungiyoyi masu zaman kansu su ƙara zuba jari wajen koyar da mata sana’o’i da samar musu da damar samun jari cikin sauƙi. Idan aka gina mace, an gina iyali; idan aka gina iyali, an gina al’umma; idan aka gina al’umma kuwa, ƙasa baki ɗaya ce za ta amfana.
Za mu ci gaba.
