Sufeto Janar Disu ya haramta wa ‘yan sanda amfani da Soshiyal Mediya ba da izini ba

Spread the love

Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu, ya umarci dukkan jami’ai da ma’aikatan Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya da su daina gudanar da duk wani aiki a kafafen sada zumunta ba tare da izini ba, yana mai gargadin cewa irin waɗannan ayyuka na iya kawo cikas ga mutunci, ƙwarewa da kuma martabar rundunar.

A cewar umarnin, an hana jami’an ’yan sanda wallafawa ko rarraba bidiyo, hotuna ko wasu bayanai ba tare da amincewar hukuma ba yayin da suke sanye da kayan aiki na ’yan sanda.

Haka kuma, an haramta musu yin tsokaci a bainar jama’a kan harkokin rundunar, fitar da bayanan sirri na ayyukan tsaro ko amfani da matsayinsu na jami’an ’yan sanda domin tallata kansu, nishaɗi ko kasuwanci.

Sufeto Janar ɗin ya jaddada cewa, duk da muhimmancin kafafen sada zumunta wajen sadarwa da hulɗa da jama’a, dole ne jami’an rundunar su yi amfani da su ne bisa ƙa’idoji da dokokin Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya.

Rundunar ta ɗauki wannan mataki ne domin kare amincewar jama’a da kuma tabbatar da ƙwararrun ayyukan rundunar acikin al’umma.

By Babaji

Leave a Reply