
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta kammala jigilar dawowar alhazan ƙasar zuwa gida daga Saudiyya, inda jirgin ƙarshe na alhazan Jihar Zamfara da ya isa a ranar 23 ga Yuni, 2026.
Kammala dawowar alhazan ya nuna rufe harkokin hajjin 2026, wanda ya nuna an samu nasarar dawo da alhazan gida lafiya da ƙasa mai tsarki.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, NAHCON ta ce akwai alhazai guda 12 da ke karɓar magani a asibitocin Saudiyya bisa wasu cututtuka mabanbanta da ke damun su. Ta ce tana sanya ido akan halin da suke ciki kuma ta shirya wa dawowarsu gida cikin aminci yayin da aka sallame su.
Shugaban hukumar, Ambasada Isma’il Abba Yusuf ya yi godiya ga Allah (SWT) busa nasarar kammala aikin hajjin na bana ba tare da samun manyan ƙalubale ba yana mai jinina wa sadaukarwa da gudumawar Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima wajen cimma hakan.
Haka kuma, NAHCON ta yaba wa haɗin hukumomin alhazan jihohin Nijeriya, masu aikin bayar da lasisin tafiye-tafiye, masu samar da sabis, abokan hulɗar sufurin jiragen sama, tawagogin lafiya, jami’an tsaro, ‘yan jarida da kuma kacokam alhazan na Nijeriya.
Tuni dai hukumar ta fara shirin gudanar da aikin Hajjin 2027 domin ganin an samu nasara a harkokinsa bayan nasarar kammala na 2026 cikin tsari.
