Tsoro mai kyau da tasirinsa ga kyawawan ɗabi’u

Spread the love

Tare da BILKISU YUSUF ALI, Ph’D

Gabatarwa:

Tsoro yana da nau’o’i biyu a rayuwar ɗan Adam. Akwai tsoro mara kyau wanda ke hana mutum ci gaba, akwai kuma tsoro mai kyau (positive fear) wanda ke taimaka wa mutum ya guji kuskure kuma ya rungumi kyawawan ɗabi’u. A cikin addini da zamantakewa, tsoro mai kyau yana taka muhimmiyar rawa wajen gina hali nagari, hana aikata laifi da kuma tabbatar da zaman lafiya a iyali da al’umma.

Ma’anar tsoro mai kyau

Tsoro mai kyau shine jin tsoron aikata abin da zai jawo fushin Allah, ko cutar da kai ko al’umma, tare da amfani da wannan tsoro wajen yin abin da ya dace.

A Musulunci ana kiran wannan da Taƙwa – wato kiyaye dokokin Allah da nisantar haram.

Hujjoji daga Alƙur’ani

Allah (SWT) Ya ce: “Ya ku waɗanda ku ka yi imani, ku ji tsoron Allah yadda ya kamata.” (Surat Ali-Imran: 102.) Haka kuma Ya ce: “Lallai mafi daraja a cikinku a wurin Allah shine mafi tsoron Allah.”  (Surat Al-Hujurat: 13.) Wannan yana nuna cewa tsoro mai kyau yana daga cikin abin da ke ɗaga darajar mutum.

Hujjoji daga hadisai

Annabi (SAW) ya ce: “Mutum mai hankali shine wanda ke yi wa kansa hisabi kuma ya yi aiki domin bayan mutuwa.” (Sunan Tirmidhi) Haka kuma, “Ku ji tsoron Allah a duk inda kuke.” (Sahih Muslim)

Ra’ayoyin masana

Imam Al-Ghazali a cikin Ihya Ulum al-Din ya ce: “Tsoron Allah shine makamin gyaran zuciya da hana mutum faɗawa cikin zunubi.” Ibn Khaldun a cikin Muƙaddimah ya bayyana cewa: “Al’umma ba za ta yi daidai ba sai da doka da tsoro mai hana zalunci.” Émile Durkheim ya ce: “ɗabi’u na al’umma suna ɗorewa ne idan akwai abin da ke takura mutane daga karya doka.”

Muhimmancin tsoro mai kyau

1. Hana aikata laifi

Mutum mai tsoro mai kyau ba ya sata ko  karya, ko cutar da wasu haka da wuya a haɗa kai da shi a cutar da wasu ko a yi aikin assha. Wannan ya sa da dama akan ɗora mata a kan waɗansu muƙami shine an san su na da tsoro.

2. Gina ladabi da mutunci

Tsoro yana sa mutum biyayya da girmama al’umma . Don haka tsaro yana sa mutum ya zama mai girmama iyaye da malamai  da shugabanni.

3. Inganta tarbiyya a iyali

Yaro da aka koya masa tsoron Allah da mutunci yana zama mai ladabi a gida. Kuna ba zai yi ha’inci ba ko sata ko wani mummunan laifi kuma ba za a haɗa kai da shi a yi ba.

4. Tabbatar da zaman lafiya

Idan mutane suna jin tsoron yin laifi, za a samu zaman lafiya a al’umma. Idon an samu  matasa masu tsoron Allah ba sa shiga rikici ko shaye-shaye. In sun samu kansu cikin shugabanci misali a siyasa, shugabanni masu tsoron Allah suna rage cin hanci da rashawa da son kai da zaluntar al’umma.

Illolin rashin tsoro mai kyau

A. Yawaitar laifuka

B. Rashin ladabi a gida da makaranta

C. Cin hanci da rashawa

D. Rashin zaman lafiya

Hanyoyin koyar da tsoro mai kyau

1. Tarbiyya tun ƙuruciya.

2. Iyaye su koya wa yara tsoron Allah da ladabi.

3. Ilimin addini

Makarantu da masallatai su ƙara koyar da darussan tsoron Allah.

4. Zama abin koyi

Iyaye da shugabanni su nuna hali nagari.

5. Nasiha da faɗakarwa

6. rika yi wa matasa wa’azi akai-akai.

Kammalawa:

Tsoro mai kyau ba tsoro na firgita ba ne, illa wata hanya ce ta gina hali nagari da kiyaye mutum daga aikata laifi. Addini da masana sun nuna cewa shine ginshiƙin kyawawan ɗabi’u da zaman lafiya a al’umma.

Saboda haka, ya zama wajibi a raya wannan ɗabi’a a cikin iyali da al’umma domin samun rayuwa mai kyau.

Manazarta:

Al-ƙur’ani mai girma

Sahih Muslim

Sunan Tirmidhi

Ihya Ulum al-Din – Imam Al-Ghazali

Muƙaddimah – Ibn Khaldun

Émile Durkheim

A. B. Fafunwa – History of Education in Nigeria (1974)

By ukarofi

Leave a Reply