27
Mar
Daga SANI AHMAD GIWA Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta a Nijeriya, INEC, ta ce ta saka ranakun da za ta bayar da takardar shaidar cin zaɓe ga zaɓaɓɓun gwamnoni a jihohin ƙasar da aka gudanar da zaɓen gwamna. A wata sanarwar da hukumar INEC ɗin ta fitar mai ɗauke da sa hannun shugaban kwamitin yaɗa labarai da ilimantar da masu kaɗa ƙuri'a na hukumar, Festus Okoye, ta ce sashe na 72 (1) na Dokar Zaɓen ƙasar ta 2022, ya ɗora wa hukumar alhakin bayar da takardar shaidar cin zaɓe ga zaɓaɓɓun 'yan takara a cikin kwana 14 da yin zaɓen.…