Labarai

Sarkin Rano ya naɗa sabon Chiroma tare da ɗaga darajar wasu dagatai biyu

Sarkin Rano ya naɗa sabon Chiroma tare da ɗaga darajar wasu dagatai biyu

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano A Kano, Mai Martaba Sarkin Rano, Ambasada Muhammad Umar Isa (Autan Bawo), ya naɗa ɗansa a matsayin Chiroman Rano, kuma Hakimin Gundumar Gwamma, tare da ɗaga darajar wasu Dagatai biyu zuwa Hakimai Masu Gunduma. An gudanar da bikin naɗin ne a fadar Sarkin da ke garin Rano ranar Juma’ar da ta gabata. Bikin naɗin ya samu halartar Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf; Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Hon. Abdurrahman Suleiman Kawu Sumaila; ɗan Majalisa mai wakiltar ƙananan hukumomin Rano, Bunkure da Kibiya, Rt. Hon. Kabiru Alasan Rurum; wakilan sarakunan Kano, Karaye…
Read More

An sake zaɓar Benjamin da Okonkwo a matsayin shugaba da babban sakataren SWAN

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Jumma'a aka kammala babban taron Ƙungiyar Maruwaita Labaran Wasanni ta Ƙasa (SWAN), inda aka sake zaɓa da rantsar da Mista Isaiah Kemje Benjamin (JP) da Amb. Ikenna Okonkwo ANIPR a matsayin shugaba da babban sakatare na wa'adin wasu shekaru uku. Taron, wanda ya samu halartar wakilai daga jihohi a sassan Nijeriya, ya kuma samar da sabuwar majalisar zartarwar (NEC), wadda aka ɗora wa alhakin kula da harkokin ƙungiyar na tsawon shekaru uku. Zaɓen, wanda aka gudanar a ranar 28 ga Agusta, 2026, ya bayar dama da kuma fage ga wakilai domin yin…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta tura allurar rigakafi 500,000 yayin ɓarkewar cutar mashaƙo a Katsina da Kano

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta tura allurar cutar mashaƙo guda 500,000 zuwa jihohin Katsina da Kano a wani yanayi na ɗaukar matakin gaggawa kan ɓarkewar cutar domin bayar da kariya acikin yara. Ma'aikatar Lafiya da Walwalar Al'umma ta Tarayya ce ta sanar da haka a wata sanarwa da fitar a ranar Juma'a. Ta ce, Hukumar kula da lamuran Ci-gaban Lafiya a Matakin Farko ta Ƙasa (NPHCDA) ce ta gudanar da aikin raba allurar ne domin bayar da tallafin harkokin rigakafi a yankunan da al'amarin ya shafa. Ma'aikatar ta ce, wannan ɓangare ne na bada agajin gaggawa…
Read More
Ku fi mayar da hankali kan buƙatun al’umma — Barista Ahmad

Ku fi mayar da hankali kan buƙatun al’umma — Barista Ahmad

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Kwamishinan ƙananan hukumomi da cigaban al’umma na Jihar Gombe, Barista Sani Ahmad Haruna, ya buƙaci sabbin shugabannin ƙananan hukumomi 11 da na yankunan cigaban ƙananan hukumomi (LCDA) 13 da su mayar da hankali kan muhimman buƙatun al’ummominsu domin samar da ci gaba mai ma’ana a yankunansu. Kwamishinan ya yi wannan kiran ne a Bauchi a lokacin da yake yi wa shugabannin ƙananan hukumomin ƙarin haske kan ayyukan ci gaba da gwamnatin jihar ke aiwatarwa. Ya ce ya kamata kowane shugaban ƙaramar hukuma ya fahimci abubuwan da al’ummarsa suka fi buƙata, sannan ya gabatar da su…
Read More

Nijeriya tana bin Togo, Nijar da Benin bashin Dala 11.16m na lantarki a 2025 – NERC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar kula da Harkokin Lantarki ta Ƙasa (NERC) ta ce akwai Dala miliyan 11.16 akan ƙasashen Togo, Nijar da Benin da Nijeriya ke bin su na bashin wutar lantarkin da kamfanonin raba lantarki na (GenCos) suka raba musu a shekarar 2025. A rahotonta na shekara-shekara, hukumar ta ce sashen gudanar da kasuwanci (MO) ya gabatar da takardun biyan kuɗaɗen lantarki ga ƙasashen na jimillar Dala miliyan 73.91, amma Dala 62.75 ne kaɗai aka biya. Rahotanni sun bayyana cewa, NERC ta zayyano ƙasashen a matsayin abokan hulɗar lantarki, waɗanda suka biya kaso 84.90 na ainihin…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Shugaban NPC, Aminu Wushishi ya rasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa (NPC), Dakta Aminu Wushishi ya rasu. Marigayin ya rasu ne a yau Juma'a, 28 ga Agusta, 2026 yayin da aka isar da labarin mutuwarsa a Minna bayan sallar Juma’a. Shugaban na NPC wanda kuma tsohon sakataren jam'iyyar PDP ne na Jihar Neja, ya rasu ne bayan wani garen rashin lafiya. Tsohon shugaban PDP na jihar, Barista Tanko Benji ne ya tabbatar da rasuwarsa marigayin ga jaridar Blueprint. "Aminu ya rasu, ina cikin fushi kuma bana cikin yanayi mai kyau yanzu," inji Benji.
Read More

Yaƙi da ta’addanci: Amurka za ta janye sojoji 200 daga Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Cibiyar Tsaron Amurka, Pentagon, ta shirya janye kimanin dakarunta guda 200 daga Nijeriya waɗanda aka tura ƙasar a wannan shekarar domin yaƙi da ƙungiyoyin "tsatstsauran ra'ayin addinin Islama", kamar yadda New York Times (NYT) ta ruwaito. Jami'an Amurka da Nijeriya sun shaida wa jaridar cewa tawagar dakarun da aka tura ta samar da sakamakon da aka yi tsammani. A cewar rahoton da NYT ta fitar a ranar Alhamis, wasu daga cikin tawagar dakarun za su cigaba da kasancewa domin cigaba da taimaka wa ayyukan leƙen asiri da horar da ƙananan jami'ai. Jami'an Amurka sun…
Read More

Sojoji sun ƙwato muggan makamai bayan halaka ‘yan ta’adda 21 a Adamawa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Dakarun Rundunar Sojin Nijeriya sun yi nasarar halaka 'yan ta'addan Boko Haram guda 21 yayin wani samame a sansaninsu da ke yankin Tsaunin Kopre na Ƙaramar Hukumar Hong a Jihar Adamawa. Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa an gudanar da atisayen ne a tsakanin 26 da 27 ga Agusta, bayan samun wani rahoton leƙen asiri da ya nuna cewa akwai mayaƙan ƙungiyar a yankin. A cewarta, sojojin sun je yankin ne a yanayi na sanɗa kafin suka ƙaddamar da hare-hare a yankin tsaunin na Kopre. Zagazola Makama ya ce atisayen ya yi…
Read More
Duwan ya zama shugaban kwamitin shirin KT1T na shiyyar Daura

Duwan ya zama shugaban kwamitin shirin KT1T na shiyyar Daura

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, Ph.D., ya amince da naɗin Hon. Shafi’u Abdu Duwan a matsayin shugaban kwamitin shirin Katsina One-Person-One-Tree (KT1T) na shiyyar Daura. Hon. Shafi’u Abdu Duwan zai jagoranci kwamitin shiyar wajen tabbatar da ingantaccen aiwatar da shirin dasa bishiyoyi miliyan 11 a yankunan da ke ƙarƙashin shiyyar Daura, tare da haɗa kai da ƙananan hukumomi, shugabannin gargajiya da na addini, mata, matasa da sauran masu ruwa da tsaki. A matsayinsa na shugaban kwamitin, zai sa ido kan yadda ake aiwatar da shirin, wayar da kan al’umma kan muhimmancin dasa da kare bishiyoyi, tare da tabbatar…
Read More

Badaƙalar hukumar bogi: ICPC ta shawarci a hukunta jami’an gwamnati 13

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ICPC, ta bayar da shawara ga Gwamnatin Tarayya kan a hukunta wasu jami'an gwamnati guda 13 bisa rawa da suka taka a badaƙalar haramtacciyar hukumar nan da aka kira da Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC). Hakan na ƙunshe ne a cikin rahoton binciken yadda, hukumar, wadda ba ta samu amincewa ba a dokance, ta samu damarmaki kan gudanar da harkokinta a ofisoshin gwamnati, tsare-tsaren kuɗaɗe da wasu damarmakin gudanarwa. Haka kuma, ICPC ta bada shawarar a gurfanar da Adeniyi Adeyemi, wanda ya gabatar da kansa a…
Read More