Labarai

Harin Filato: Tilas maharan su fuskanci hukunci – Buhari

Harin Filato: Tilas maharan su fuskanci hukunci – Buhari

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ce wajibi ne maharan da suka kai mummunan hari a ƙauyukan Kanam da Wase a jihar Filato su fuskanci hukuncin abin da suka aikata, tare da bayyana harin a matsayin ƙololuwar ƙeta ga jama'a. Mai Magana da Yawun Buhari, Garba Shehu ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya bayar a ranar Talata. Shehu ya ce, Buhari ya bada umarnin “Kada a sassauta musu, kuma babu yafiya." KARANTA: INEC ta gano rijistar katin zaɓe mara kyau sama da miliyan 1.3 Ya ƙara da cewa, Buhari ya umurci hukumomin da lamarin ya shafa…
Read More
INEC ta gano rijistar katin zaɓe mara kyau sama da miliyan 1.3

INEC ta gano rijistar katin zaɓe mara kyau sama da miliyan 1.3

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce, ta gano rijistar katin zaɓe mara kyau guda 1,390,519 da aka yi a shirin rijisar katin zaɓen (CVR) da ke gudana a halin yanzu. Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka ga manema labarai ranar Laraba a Abuja, yana mai cewa wannan adadi daidai yake da kashi 45 na katin zaɓe 2,523,458 da aka kammala yin rijistarsu. Yakubu ya ƙara da cewa, wannan adadi ɓangare ne na rijistar da aka kammala daga Yunin 2021 zuwa 14 ga Janairun 2022. KARANTA: ‘Yan fashin daji sun yi awon gaba da…
Read More
‘Yan fashin daji sun yi awon gaba da ɗaliban Zamfara

‘Yan fashin daji sun yi awon gaba da ɗaliban Zamfara

Daga BASHIR ISAH 'Yan bindiga sun sace ɗalibai huɗu na Kwalejin Nazarin Kimiyyar Lafiya ta Jihar Zamfara da ke garin Tsafe, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Tsafe. Jaridar SpyeNews ta samu tabbacin aukuwar hakan daga majiyoyi daban-daban, cewa wasu 'yan fashin daji sun afka garin Tsafe ran Talata da daddare inda suka kwashi ɗaliban kwalejin ciki har da ɗalibai mata da ke zama a wajen makaranta. Majiyarmu ta ce ɗalibai biyar ne aka sace amma daga bisani ɗaya daga ciki ya kuɓuta sai ɓarayin suka tafi da mutum huɗu. Idan za a iya tunawa, ko 'yan kwanakin da suka gabata sai da…
Read More
Dattijo mai bibiyar Manhaja

Dattijo mai bibiyar Manhaja

Jaridar Blueprint Manhaja ta samu karɓuwar da hatta dattawa ma ba a bar su baya wajen bibiyarta ta. Wani dattijo na karanta Manhaja a dandalin saida jaridu na Wunti da ke cikin garin Bauchi ranar Litinin. HOTO: Khalid Idris Doya
Read More
2023: Tinubu ya mayar da martani ga Osinbajo

2023: Tinubu ya mayar da martani ga Osinbajo

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jagoran jam’iyyar APC na ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya mayar da martani kan sanarwar da mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo ya yi a kwanakin baya. Farfesa Yemi Osinbajo wanda ya shafe sama da shekaru 7 a matsayin mataimakin shugaban ƙasar Nijeriya a ranar Litinin, ya bayyana cewa, zai tsaya takarar neman tikitin zama shugaban ƙasa na jam'iyyar APC a 2023. Sanarwar da ya fitar ta kawo cikas ga tafiyar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wanda ke ganin bai kamata mataimakin shugaban ƙasar ya yi hakan ba kuma sun…
Read More
Gwamnati ta bada hutun kwana biyu albarkacin bikin Ista

Gwamnati ta bada hutun kwana biyu albarkacin bikin Ista

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta bada hutun kwana biyu albarkacin bikin Ista na bana, wato Juma'a 15 da kuma Litinin 18 ga Afrilun 2022. Babban Sakataren Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida, Dr. Shuaib Belgore ne ya bada sanarwar hutun a madadin Ministar, Rauf Aregbesola. Rauf ya buƙaci al'ummar kirista a faɗin Nijeriya da su yi amfani da wannnan lokaci na Ista wajen ɗabaƙa halin son juna, zama tare, taimakekeniya, yafiya, kyautatawa da kuma zaman lumana da haƙuri da juna kamar dai yadda Annabi Isa ya karantar a halin rayuwarsa. Kazlaika, Ministan ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga…
Read More
Yadda Xi ke ziyarar aiki a ƙauyen Maona

Yadda Xi ke ziyarar aiki a ƙauyen Maona

Daga CMG HAUSA Jiya Litinin da yamma, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aiki ƙauyen Maona, dake birnin Wuzhishan a lardin Hainan na ƙasar Sin, domin kara fahimta kan yadda ake inganta sakamakon da aka samu a fannin kawar da talauci a ƙauyen, da kuma ci gaba da aikin farfado da ƙauyen. Cikin shekarun ke nan, an dukufa wajen kyautata muhallin ƙauyen Maona, domin raya harkokin yawon shakatawa, ta yadda zai kasance abun koyi a fannin neman farfaɗowar ƙauyuka a ƙasar Sin. Mai fasarawa: Maryam Yang
Read More
‘Yan daba sun kashe wani malamin jami’a a Jos

‘Yan daba sun kashe wani malamin jami’a a Jos

Daga HABU ƊAN SARKI Wasu yara matasa ɗauke da makamai sun kashe wani malamin Jami'ar Tarayya da ke Gashua a Jihar Yobe, Muhammad Sani Mazadu, ta hanyar harbin sa da bindiga, yayin wani rikicin ýan daba a Anguwar Rogo da ke cikin garin Jos, ranar Litinin da maraice daidai lokacin da al'ummar Musulmi ke buɗa bakin azumin Ramadan na goma da suka kai. Rahotanni sun bayyana cewa, marigayin wanda magidanci ne da ke da yara uku, ya rasu ne a Babban Asibitin Koyarwa na Jami'ar Jos (JUTH), inda aka garzaya da shi, don ceton ransa daga harbin harsashin da aka…
Read More
Sanata Abdullahi Adamu ya yi murabus

Sanata Abdullahi Adamu ya yi murabus

Daga BASHIR ISAH Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya yi murabus daga matsayin sanata mai wakiltar shiyyar Nasarawa ta yamma a jihar Nasarawa. Haka shi ma mataimakinsa na Arewa, Abubakar Kyari, ya yi murabus a matsayin sanata mai wakiltar Borno ta Arewa. A yau Talata Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya karanta wasiƙun ajiye muƙaman sanatocin biyu yayin zaman majalisar. Waɗanda lamarin ya shafa sun ajiye muƙaman nasu ne biyo bayan nasarar da suka samu na zama shugabannin jam'iyyarsu ta APC a matakin ƙasa. Kafin wannan lokaci, Sanata Adamu shi ne shugaban kwamitin harkokin noma da…
Read More
Buhari ya tsawaita shekarun ritaya ga malamai a Nijeriya

Buhari ya tsawaita shekarun ritaya ga malamai a Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan dokar tsawaita shekarun ritayar malamai a Nijeriya. Babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Garba Shehu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a. A ranar 20 ga Janairu, 2021, Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da wani ƙudirin doka da ke neman ƙara shekarun yin ritaya da kuma shekarun hidimar malamai. Jigon ƙudirin dokar dai shi ne bayar da goyon baya a shari’a don amincewa da sabon shekaru 65 na ritaya daga shekaru 60 ga malaman da kuma…
Read More