2023: Tinubu ya mayar da martani ga Osinbajo

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Jagoran jam’iyyar APC na ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya mayar da martani kan sanarwar da mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo ya yi a kwanakin baya.

Farfesa Yemi Osinbajo wanda ya shafe sama da shekaru 7 a matsayin mataimakin shugaban ƙasar Nijeriya a ranar Litinin, ya bayyana cewa, zai tsaya takarar neman tikitin zama shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a 2023. Sanarwar da ya fitar ta kawo cikas ga tafiyar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wanda ke ganin bai kamata mataimakin shugaban ƙasar ya yi hakan ba kuma sun saɓa wa burin shugabancinsa.

Tinubu wanda ya kira taro da gwamnonin APC a ranar litinin, sa’o’i kaɗan bayan sun gana da mataimakinsa, ya bayyana cewa, ya gana da gwamnonin ne domin haɗa kai a kan burinsa na 2023.

Da ya ke mayar da martani ga sanarwar mataimakin shugaban ƙasa, Tinubu ya mayar da martani ga tambayar wani ɗan jarida da ya tambayi ra’ayinsa tunda Farfesa Osinbajo shine ‘Ɗansa’.

A cikin gaggawar da shugaban na APC ya mayar, ya ce: “Ba ni da wani dan da ya kai girman da zai iya yin irin wannan sanarwa”

“Burina a nan shi ne in nemi haɗin kai, goyon baya, da ƙarfafa wa jam’iyyata ta APC, burina na zama shugaban tarayyar Nijeriya a matsayin wanda zai maye gurbin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari bayan wa’adinsa,” inji shi.

Gwamnan Jihar Kebbi kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin (PGF), Atiku Bagudu, ya kuma musanta ikirarin da Osinbajo ya yi na cewa ya haɗa shi da ubangidansa na siyasa.

A cewarsa, lamarin ya nuna ingancin mutanen da ke cikin jam’iyyar APC mai mulki.

“Kasancewar muna da mutane a cikin jam’iyyarmu da ke nuna sha’awar shugabancin jam’iyyar zuwa matsayi mafi girma a fagen zaɓe ya nuna irin yadda wannan jam’iyyar tamu ta yi wa ’yan Nijeriya da ’yan jam’iyyarmu,” inji gwamnan.