Daga ABDULLAHI YAHAYA MAIƊARE
Akwai masu ganin cewa, da zarar mutane suna son junansu, to za a zauna lafiya idan suka yi aure, wanda a zahirance ba haka abun yake ba.
Masoyan da suka tsananta son junansu ma ba su cika daɗewa ba idan sun yi aure, saboda ita soyayyar kaɗai suka saka a gaba ba tare da fahimtar akwai abubuwan da suka fi soyayya muhimmanci ba a zaman aure.
Ga wasu abubuwa nan guda 10 idan ma’aurata har ma da masoya za su shigo da su cikin soyayyar su, za su zauna lafiya da juna:
- Yarda:
Duk ma’auratan da ba su amince wa junansu ba, duk yadda suke son junansu ba za su zauna lafiya da juna ba. Yarda da amince wa juna ya fi soyayyar juna tasiri a rayuwar aure. - Tausayawa juna:
Duk soyayyar da babu tausaya wa juna shirme ce. Idan ma’aurata suna burin zaman aure na har abada, dole ne su riqa tausaya wa junansu a duk lokacin da guda yake cikin abun a tausaya masa ko mata. - Haƙuri da juna:
Haƙuri da juna shi ne kan gaba wajen inganta zaman aure. Duk irin soyayyar da ma’aurata za su yiwa junansu, muddin ba za su iya haƙuri da juna ba, to babu inda aurensu zai je. - Yi wa juna uzuri:
Dole ne ma’aurata su riƙa yiwa junansu uzuri idan suna burin samun zaman lafiyar aurensu. Tsananin soyayya babu uzuri ba zai samar da zaman aure mai ɗorewa ba. - Kyakkyawan zato:
Dole ne ma’aurata su cire duk wani zargi a junansu, idan suna son zaman aurensu ya yi inganci. Duk wata soyayyar da za a surka ta da zargi babu inda za ta je.