25
Jan
Daga jaridar Manhaja Shugaban Kungiyar Miyetti Allah na Jihar Oyo Ibrahim Abubakar Jiji, ya yi korafin halin da ake ciki mambobinsu na zaman dar-dar ne a jihar biyo bayan harin da wasu matasa da ba a san ko su wane ne ba suka kai wa Sarkin Fulani Salihu Abdulkadir a yankin Igangan, a Juma’ar da ta gabata. Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Jihar Ondo ta bai wa Fulani makiyaya a jihar wa’adin kwana 7 a kan su fice mata daga dazuzzukanta. Gwamnatin Jihar Ondo ta ci gaba da kallon matakin da ta dauka a matsayin abin…
