Labarai

Yadda mafarauci ya hallaka ahalinsa a Anambra

Yadda mafarauci ya hallaka ahalinsa a Anambra

Daga WAKILINMU Rahotanni daga yankin Amanuke a karamar hukumar Awka ta Arewa a jihar Anambra, sun nuna wani mafarauci mai suna Uchechukwu Nweke, ya harbe matarsa Mrs Patricia da bindiga har lahira sannan ya banka wa gidansu wuta tare dansa Mr Obinna a ciki a bisa dalilan da ba a kai ga ganowa ba. Mai magana da yawun 'yan sandan jihar CSP Haruna Muhammed ya tabbatar da aukuwar lamarin. Inda ya ce wanda ake zargi, ya aikata ta'asar ne a safiyar Alhamis, 28 ga Janairun 2021 kana daga bisani shi ma ya harbe kansa. CSP Muhammed ya ce, "'Yan bijilantin…
Read More
Inganta fannin lafiya shi ya fi muhimmanci ga Nijeriya bisa ga sayo rigakafin korona – Gates

Inganta fannin lafiya shi ya fi muhimmanci ga Nijeriya bisa ga sayo rigakafin korona – Gates

Daga FATUHU MUSTAPHA Hamshakin dan kasuwar nan na Kasar Amurka, Bill Gates, ya shawarci Nijeriya da ta karkatar da hankalinta zuwa ga inganta fannin lafiyarta maimakon kashe makudan kudade wajen sayo allurar rigakafin cutar korona. Gates ya ba da shawar ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai ta bidiyo a Talatar da ta gabata, inda ya yi kira ga Nijeriya da kada ta yi amfani da 'yan kudaden da ta ware don kula da fannin lafiyarta wajen sayen rigakafin COVID-19 mai tsadar gaske. Jaridar Manhaja ta kalato dan kasuwar na cewa, “Ina mai bada shawarar a bai wa…
Read More
Za a fara allurar rigakafin korona a Nijeriya cikin Maris

Za a fara allurar rigakafin korona a Nijeriya cikin Maris

Daga AISHA ASAS, Abuja Gwamnatin Tarayya ta ce, ana sa ran a soma allurar rigakafin cutar korona ya zuwa karshen Maris ko Afrilun 2021.Ministan Lafiya, Osagie Ehanire ne ya bayyana haka sa'ilin da Kwamitin Shugaban Kasa Kan Yaki da COVID-19 (PTF) ke gabatar da bayanin ayyukankasa, Litinin da ta gabata a Abuja. Ehanire ya ce, "Adadin maganin da Nijeriya ta yi odar sa ta AVATT na Hukumar Hada Kan Afirka, ya danganci daidai adadin da ake bukata ne don gundun barna." Ya ci gaba da cewa, Nijeriya na yin dukkan maiyiwuwa don tabbatar da an yi wa akalla kashi 70…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta kama hanyar kula da ilimin yara marasa galihu

Gwamnatin Tarayya ta kama hanyar kula da ilimin yara marasa galihu

Daga UMAR M. GOMBE a Abuja Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya wakilta Ma'aikatar Jinkai da Agaji da Kyautata Rayuwa ta Kasa, kan ta kula da shirin gwamnati na kokarin kula da yaran da suka daina tafiya makaranta a fadin kasa. Da yake kaddamar da kwamitin mutum 18 da zai ja ragamar shirin a Talatar da ta gabata, Shugaba Buhari ya bayyana cewa ba daidai ba ne ganin yara suna gararamba a tituna da kasuwanni da sauran wurare, ba tare da suna zuwa makaranta ba. Kwamitin zai yi aikinsa ne karkashin jagorancin Ministar Jinkai da Agaji Hajiya Sadiya Umar Farouq tare…
Read More
Cutar korona: NOA ta bukaci ‘yan Nijeriya su ba da hadin kai game da allurar riga-kafin korona

Cutar korona: NOA ta bukaci ‘yan Nijeriya su ba da hadin kai game da allurar riga-kafin korona

Daga FATUHU MUSTAPHA Hukumar Wayar da Kan 'Yan Kasa ta yi kira ga 'yan Nijeriya da su daina yarda da ra'ayoyi mara tushe da ake yadawa dangane da allurar riga-kafin cutar korona kan cewa maganin na tattare da wasu illoli.  Babban Daraktan hukumar, Garba Abari ne ya yi wannan kira a lokacin bayanin kore zargin da wasu ke yi cewa ana so a yi amfani da allurar ne wajen takaita yawan al'umma, lamarin da Abari ya ce ba gaskiya ba ne. Yana mai cewa, "Babu wata allurar riga-kafin da za a bari a shigo da ita Nijeriya ko a yi…
Read More
Kotu ta dage shari’ar El-Zakzaky zuwa 8 ga Maris

Kotu ta dage shari’ar El-Zakzaky zuwa 8 ga Maris

Kotu ta dage shri'ar El-Zakzaky zuwa 8 ga watan Maris Daga AISHA ASAS A Talatar da ta gabata babbar Kotun Jihar Kaduna da ke shari'ar jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya Ibrahim El-Zakzaky da matarsa  Zeenat, ta dage ci gaba da shari'ar ya zuwa ranar 8 da 9 ga watan Maris mai zuwa. Kotun ta dage shari'ar ne biyo bayan hukuncin da Alkali Gideon Kurada ya yanke dangane da neman kotu ta ba shi lokaci da lauyan El-Zakzaky Mr Femi Falana ya yi a bisa wakilcin Mr Eddie Inegedu, domin ba shi damar nazarin wani bidiyo da wasu shaidu biyu suka…
Read More
Matsalar Tsaro: Makarfi ya gargadi ‘yan Nijeriya

Matsalar Tsaro: Makarfi ya gargadi ‘yan Nijeriya

Daga Aisha Asas Tsohon gwamnan Jihar Kaduna Sanata Ahmed Mohammed Makarfi, ya ja hankulan 'yan Nijeriya a kan su daina barin son zuciyarsu yana tasiri wajen daukar matakai wanda hakan ka iya haifar da rikici. Makarfi ya nuna bukatar da ke akwai 'yan Nijeriya su fahimci cewa matsalar tsaron da ke addabar kasar nan aba ce da ke bukatar a yi mata taron dangi domin dakile ta. Yana mai cewa, "Wannan matsala ce da ta shafe mu baki daya." Makarfi ya yi wadannan bayanan ne a wata sanarwa da ya fitar inda ya nuna damuwarsa kan tabarbarewar sha'anin tsaron Nijeriya.…
Read More
Rikicin FCC: Kwamishinoni sun ja shugabar hukuma zuwa ICPC

Rikicin FCC: Kwamishinoni sun ja shugabar hukuma zuwa ICPC

Daga jaridar Manhaja Kwamishinoni masu wakiltar jihohi 36 na kasar nan hada da birnin tarayya Abuja, tare da Hukumar Kyautata Da'ar Ma'aikata ta Kasa (FCC) sun rubuta takardar korafi a kan shugabar hukumar FCC Dr. Muheeba Fraida Dankaka zuwa ga Hukumar Yaki da Rashawa da Laifuka Masu Alaka da Rashawa (ICPC) bisa zarginta da yin ba daidai ba da matsayinta. Takardar korafin mai dauke da kwanan wata 18/1/2021 wadda ta sami sa hannun Sir Augustine Wokocha da Abdul Wasiu Bawa-Allah, ta nuna yadda shugabar FCC ta mamaye komai na hukumar sannan ta karbe ayyukan kwamishinonin tana mika wa daraktocinta tare…
Read More
‘Yan-bindiga sun kai hare-hare a sassan Neja

‘Yan-bindiga sun kai hare-hare a sassan Neja

Daga jaridar Manhaja 'Yan-bindiga sun kai hare-hare a wasu kauyukan karamar hukumar Paikoro da ke Jihar Neja, inda suka hallaka mutum shida tare da yin garkuwa da mutum biyar sannan suka jikkata sama da mutum 20. Bayanai daga jihar sun nuna 'yan-bindigar sun soma ta'addacinsu ne daga Asabar da ta gabata zuwa washegari Lahadi da rana. Wani mazaunin daya daga cikin kauyukan da harin ya shafa mai suna Abubakar Azaido, ya shaida wa Manhaja ta tarho cewa sama da mutum 20 da suka jikkata a harin aka kai babbar asibitin Kafin Koro. Ya ce, akalla mutum 3000 ne suka tsere…
Read More