01
Feb
Daga AISHA ASAS Gwamnan Jihar Barno, Babagana Umara Zulum, ya ƙalubalanci sabbin shugabannin tsaro da su assasa kyakkyawar alaƙar aiki a tsakaninsu da ƙasashen da Nijeriya ke maƙwabtaka da su, wato Chadi da Kamaru da kuma Nijar. Kazalika, ya shawarci manyan hafsoshin da su kasance masu haƙuri da kuma sauraron jama'a a halin aiwatar da ayyukansu. Gwaman ya faɗa wa jami'an haka ne sa'ilin da ya karɓi baƙuncinsu a fadar gwamnatin jihar a Lahadin da ta gabata yayin da suka yi ziyarar aiki ta farko a jihar. Shugaban tsaro Major-General Leo Irabor, shi ne ya jagoranci takwarorinsa Major-General Ibrahim Attahiru…
