Buhari ya jaddada bukatar hadin kan kasashen duniya wajen magance matsalolin duniya

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jaddada bukatar da ke akwai na kasashen duniya su hada kawunansu su yaki annobar korona da sauran manyan matsalolin da suka addabi duniya.

Buhari ya yi wannan furuci ne a fadarsa da ke Abuja, sa’ilin da yake karbar wasikun shaida daga sabbin jakadun Masar da Saudiyya da kuma Argentina a Nijeriya.

A cewarsa, “Matsaloli iri guda ne ke ci wa kasashenmu tuwo a kwarya, ciki har da matsalar ta’addanci da tabarbarewar tsaro da sauyin yanayi da karuwar yawan al’umma da safarar mutane da rashawa da talauci da kuma safarar makamai manya da kanana.

“Bayan dukkan wadannan, sai kuma ga cutar korona ta kunno kai a karo na biyu. Wadannan matsaloli na bukatar a hada kai wajen samar da sahihan hanyoyin magance su.”

Haka nan, Shugaba Buhari ya nuna gamsuwarsa dangane da kyakkyawar alakar da ke tsakanin Nijeriya da kashen uku, musamman kasancewar Nijeriya da takwarorin nata na tarayya wajen mu’amalantar juna ta hanyoyi daban-daban.

Jakadun da lamarin ya shafa su ne; Mr Ihab Moustafa Awad Moustafa mai wakiltar kasar Masar, sai Mr Faisal Ebraheem Alajrafi Alghamdi mai wakiltar Saudiyya da kuma Mr Alejandro Miguel Francisco Herrero daga kasar Argentina.