Bankwana: Buratai ya zayyano nasarorin da ya samu a tsakanin watanni 66

Daga AISHA ASAS

Tsohon Babban Hafsan Hafsoshin Nijeriya, Lt. Gen. Tukur Yusuf Buratai ya ce, watanni 66 da ya shafe a matsayin shugaban rundunar sojoji abin a yaba ne. Ya ce, a zamaninsa fannin sojin kasar nan ya samu nasarori da daman gaske tsakanin 2015 zuwa Janairun 2021.

Buratai ya fadi haka ne a jawabinsa na bankwana da ya yi yayin da yake mika ragamar aiki ga magajinsa Maj. Gen Ibrahim Attahiru, a Alhamis da ta gabata a Abuja.

Kafin nada Attahiru a matsayin sabon shugaban sojojin Nijeriya da Shugaba Buhari a Talatar da ta gabata, Buratai ya kasance Babban Hafsan Hafsoshi wanda ya fi kowanne dadewa rike da wannan mukami.

A jawabin nasa Buratai ya ce, aikin soja ya inganta a karkashinsa, sojoji sun kasance masu kwazo wajen aiwatar da ayyukansu na bai wa kasa tsaro yadda ya kamata. Sauran nasarorin da ya ce an samu sun hada da; samar da kayayyakin aiki da gina sabbin barikin sojoji tare da yi wa tsaffin kwaskwari, gina makarantu da asibitoci da sauransu.

Game da sha’anin ingan tsaro kuwa, ya ce an yi nasarar karya lagwan Boko Haram, sannan sojoji sun yi nasarar kwato wasu garuruwan da ke hannu ‘yan bindiga a yankin Arewa maso-gabas. Tare da cewa, kusan an ci karfin matsalar tsaro a zamanin jagorancinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *