Majalisa na sane da nadin sabbin shugabannin hafsoshin da Buhari ya yi – Fadar Shugaban Kasa

Adaga FATUHU MUSTAPHA

Fadar Shugaban Kasa ta sanar cewa sabbin shugabannin sojojin da aka nada kwanan nan za su bayyana gaban Majalisar Dattawa domin tabbatar da nadin nasu.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, Hadimin Shugaba Buhari Kan Harkokin Majalisar Tarayya (Bangaren Dattawa), Sanata Babajide Omoworare ya bayyana cewa, tuni Shugaba Buhari ya tura wasika ga Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan, yana mai bukatar a tabbatar da nadin wadanda lamarin ya shafa.

Sanarwar ta nuna cewa: “Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da Majalisar Tarayya nadin da ya yi tare da neman majalisar ta tabbatar da nadin nasa a wata wasika da aike da ita mai dauke da kwanan wata 27, ga Janairun 2021.

“Buhari ya yi hakan ne daidai da dokar soji sashe na 18 (1) kamar yadda yake kunshe cikin Kundin Dokokin Kasa.

“Sabanin yadda wasu ke ra’ayin cewa Buhari ya bi ta kofar baya wajen yin nadin ba tare da sanin Majalisar Tarayya ba, da kuma cewa, ba shi da niyar neman yardar majalisar wajen tabbatar da nadin.

“Bayan nadin, Buhari ya nemi yardar Majalisar Dattawa don ta tabbatar da Major General Lucky Irabor da Major General Ibrahim Attahiru da Rear Admiral Awwal Gambo da kuma Air Vice Marshal Isiaka Amao a kan mukaman da aka nada su.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *