Buratai ya yi gargaɗi kan katsalandan ɗin ƙasashen waje a batun Tinubu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon Shugaban Rundunar Sojojin Nijeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai (mai ritaya), ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su yi tsayuwa tsayin daka wajen kare ikon mulkin ƙasar, tare da yin watsi da duk wani yunƙurin tsoma bakin ƙasashen waje cikin harkokin cikin gida.

Kiran na Buratai ya biyo bayan matakin da ake ƙoƙarin ɗauka na fitar da wasu takardu da ake zargin suna da alaƙa da binciken safarar miyagun ƙwayoyi da ya shafi Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ake cewa binciken ya samo asali ne tun kimanin shekaru 33 da suka gabata.

Sai dai tsohon shugaban sojojin ya nuna rashin amincewarsa da yadda lamarin ke tasowa, yana mai cewa bai kamata zargin da ake yi ya zama sanadin bata sunan Nijeriya ko tauye martabar ƙasar a idon duniya ba.

Buratai ya bayyana matsayinsa ne a wani rubutu mai taken “Fifita Nijeriya: Kare Ikon Mulki Da Martabar ƙasa – Ra’ayi Na Kishin ƙasa Ba Tare Da ɓangaranci Ba”, wanda ya wallafa a shafinsa na Facebook da aka tabbatar da sahihancinsa.

Rahotanni sun ce wata Kotun Gundumar Tarayya ta Amurka da ke Washington, D.C. ta bai wa Shugaba Tinubu, Hukumar Bincike ta Tarayya ta Amurka (FBI) da kuma Ma’aikatar Shari’a ta Amurka wa’adin zuwa 28 ga Agusta, 2026, domin su nuna adawa da sakin wasu takardu da ake danganta su da binciken.

Buratai ya ce, saɓanin yadda wasu ke kallon lamarin a matsayin batun da ya shafi Shugaba Tinubu kaɗai, abin ya fi haka girma, domin duk wani bayani da aka fitar na iya yin tasiri ga Nijeriya da ’yan ƙasarta.

Ya ce: “Wannan ba batun Bola Tinubu kaɗai ba ne; batun ’yan Nijeriya miliyan 250 ne, waɗanda alfahari da ƙasarsu, makomar tattalin arzikinsu da matsayinsu a idon duniya ke cikin haɗari.”

Tsohon babban hafsan sojojin ya ce ya kamata ’yan Nijeriya su damu da irin tasirin da kafafen yada labarai na duniya za su iya yi idan aka saki takardun.

A cewarsa, idan kafafen yaɗa labarai suka fara rubuta kanun labarai kan “Shugaban Nijeriya da ake alaƙanta shi da zargin miyagun awayoyi”, duniya ba za ta raba batun mutumin da ƙasar da yake jagoranta ba.

Buratai ya ce: “Idan duniya ta karanta kanun labarai kan ‘Shugaban Nijeriya’ da ake alaƙanta shi da zargin miyagun ƙwayoyi, ba za su raba mutumin da ƙasa ba. Za su ga Nijeriya. Za su ga ’yan Nijeriya.”

Ya kuma yi jayayya cewa zargin da ake magana a kai ya samo asali ne tun kimanin shekaru 33 da suka wuce, don haka bai kamata a yi amfani da shi shi kaɗai wajen tantance dukkan tarihin siyasar Tinubu ba.

Ya tambayi ko akwai wani ɗan Nijeriya da zai iya cewa mutum baya canzawa bayan shekaru 33, ko kuma kasa za ta rika hukunta shugabanninta bisa ayyukan da suka yi a lokacin kuruciyarsu ba tare da la’akari da shekarun da suka biyo baya na hidima ba.

Buratai ya ce, ya kamata a kuma yi la’akari da tarihin siyasar Tinubu, musamman lokacin da ya kasance gwamnan Jihar Legas da kuma rawar da ya taka daga baya a siyasar aasa, wajen tantance irin gudunmawarsa ga ci gaban Nijeriya.

Tsohon hafsan sojojin ya kuma tambayi ko ya dace wata kotun ƙasashen waje ta riƙa yanke hukunci kan martabar shugaban ƙasa mai ci, wanda miliyoyin ’yan Nijeriya suka zaɓa.

Ya ce Nijeriya tana da hukumomin cikin gida da tsarin dimokuraɗiyya da za su iya magance tambayoyi da suka shafi shugabanninta.

“Ba mu zabi kotun Amurka domin ta tantance shugabanninmu ba. Ba mu nemi FBI ta tantance halin shugaban ƙasarmu ba,” inji shi.

Buratai ya buƙaci ’yan siyasar Nijeriya da kada su mayar da batun makamin siyasa ko taƙaddamar ɓangaranci, yana mai cewa maslahar ƙasa ya kamata ta kasance a gaba da muradun jam’iyya.

Ya yi gargaɗin cewa sakin takardun na iya samun illa ga tattalin arziki, musamman idan masu zuba jari na ƙasashen waje suka ɗauki taƙaddamar a matsayin alamar rashin zaman lafiyar siyasa.

Ya ce hakan na iya shafar zuba jarin kasashen waje kai tsaye, haɗin gwiwar ci gaba da ƙasa da kasa, kuɗaɗen da ’yan Nijeriya mazauna kasashen waje ke turawa gida, yawon buɗe ido da harkokin kamfanonin Nijeriya a ƙasashen waje.

“Waɗannan ba damuwa ce ta zato kawai ba; barazana ce ta hakika da za ta iya shafar rayuwar talakawan Nijeriya,” ya bayyana.

By ukarofi

Leave a Reply