’Yan sanda sun gano wajen sayar da jarirai a Ogun

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar ’yan sandan Jihar Ogun ta gano wata cibiyar haihuwar jarirai da ake zargin ana gudanar da safarar mutane da kuma sayar da yara a yankin Mowe na jihar.

A yayin samamen da aka gudanar a ranar Litinin, ’yansandan sun ceto mata biyu masu juna biyu da yara huɗu, tare da cafke mutum shida da ake zargi da hannu a lamarin.

Kakakin rundunar, DSP Oluseyi Babaseyi, ya ce an kai samamen ne a wani gida da ke Abaren ɓillage, Mowe, bayan samun bayanan sirri kan ayyukan safarar mutane da kuma ba da yara ba bisa ka’ida ba.

Ya ce matan da aka ceto sun hada da Foluke Ilesanmi, mai shekaru 23, wadda ke da cikin wata bakwai, da Melody Ejekwa, mai shekaru 20, mai cikin wata takwas.

Haka kuma, ’yan sandan sun ceto yara maza biyu da mata biyu, tare da kama wadanda ake zargi shida, ciki har da wata ma’aikaciyar jinya.

Rundunar ta ce bincike ya kai jami’anta wani asibiti a Mowe, inda suka gano wata mata mai suna Blessing Bright Effiong, mai shekaru 26, wadda ta haihu a ranar 20 ga Agusta, amma ba a gano inda jaririnta yake ba.

‘Yan sandan sun ce an kama ma’aikaciyar jinyar da ke kula da matar domin taimakawa wajen gano jaririn.

An miƙa lamarin ga Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar da ke Eleweran, Abeokuta, domin ci gaba da bincike da gano sauran wadanda ke da hannu a zargin safarar mutane da sayar da jarirai.

By ukarofi

Leave a Reply