Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
A Kano, Mai Martaba Sarkin Rano, Ambasada Muhammad Umar Isa (Autan Bawo), ya naɗa ɗansa a matsayin Chiroman Rano, kuma Hakimin Gundumar Gwamma, tare da ɗaga darajar wasu Dagatai biyu zuwa Hakimai Masu Gunduma. An gudanar da bikin naɗin ne a fadar Sarkin da ke garin Rano ranar Juma’ar da ta gabata.
Bikin naɗin ya samu halartar Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf; Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Hon. Abdurrahman Suleiman Kawu Sumaila; ɗan Majalisa mai wakiltar ƙananan hukumomin Rano, Bunkure da Kibiya, Rt. Hon. Kabiru Alasan Rurum; wakilan sarakunan Kano, Karaye da Gaya; kwamishinoni; masu ba Gwamna shawara; shugabannin ƙananan hukumomi; da sauran Hakimai da Dagatai.
Da yake jawabi bayan naɗin, Sarkin Rano ya bayyana cewa an yi wannan naɗi ne duba da yadda waɗanda aka naɗa ke gudanar da mu’amalarsu da al’umma, da kuma irin gudunmawar da suke bayarwa ga Masarautar Rano.
Ya kuma yi kira gare su da su yi amfani da damar da suka samu da kuma gagarumar damar da suke da ita wajen hidimtawa al’umma, tare da jan hankalinsu da su zauna da al’ummar da suke mulka lafiya, da kuma kawo musu abubuwan da za su kawo ci gaba a yankunansu.
Sarkin ya nuna jin daɗinsa tare da yabawa Gwamnan Jihar bisa damar da ya samu na halartar bikin naɗin da kuma shaida daurin auren ɗan Sarkin da aka naɗa Chiroma. Ya kuma gode wa Gwamnan bisa yadda yake samar da muhimman ayyuka a yankin domin ci gaban al’ummar wannan Masarauta.
A nasa bayanin, Gwamnan Jihar, Alhaji Abba Kabir Yusuf, baya ga taya sabbin Hakiman murnar naɗin da aka yi musu, ya ce gwamnatin jihar na ƙoƙarin ganin Masarautar Rano ta samu ingantaccen ruwan sha, inda ya ce tuni aka samu wurin gudanar da aikin tare da bayar da kwangilar aikin.
Ya kuma ce gwamnati na ƙoƙarin samar da hanyoyi domin inganta harkokin sufuri a yankin.
Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatin tasa ta amince da ɗaga darajar asibitin yankin zuwa babban asibitin gwamnatin tarayya, tare da mayar da Makarantar Koyar da Aikin Gyaran Gida da Ci gaban Birane zuwa Babbar Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta ƙasa (Federal Polytechnic), wanda ɗan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kano ta Kudu, Hon. Abdurrahman Suleiman Kawu Sumaila, ya sanya hannu daga gwamnatin tarayya.
Inda ya ce wannan ba ƙaramin ci gaba ba ne da yankin da ma Jihar Kano suka samu. Ya kuma bayyana cewa tsohuwar makarantar gwamnatin jihar za a mayar da ita zuwa garin Sanatan, wato Sumaila.
A wani ci gaba kuma, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar wa Sarkin Rano, Ambasada Muhammad Umar Isa, cewa gwamnatin jihar ta amince masa da zama Amirul Hajji na shekarar 2027, duba da gogewarsa da ƙwarewarsa a harkokin yau da kullum.
Waɗanda aka naɗa sun haɗa da Abubakar Muhammed Isa Umar, a matsayin sabon Chiroman Rano kuma Hakimin Gundumar Gwamma; Isma’il Usman Muhammad Kibiya, wanda aka ɗaga darajarsa daga Dagacin Hammar zuwa Hakimin Gundumar Hammar; da kuma Nura Abdulkadir Ja’e, a matsayin Katikan Rano kuma Hakimin Gundumar Durba.
Da suke mayar da jawabi bayan naɗin nasu, Hakiman sun nuna jin daɗinsu tare da tabbatar wa Sarkin cewa za su yi amfani da damar da aka ba su wajen ciyar da Masarautar gaba da kuma haɗa kan al’ummar yankunansu.
Kazalika, sun gode wa Sarkin bisa ɗaga darajarsu zuwa Hakimai Masu Gunduma, inda suka ce hakan ba ƙaramin nasara ba ne a tarihin rayuwarsu. Hakiman sun kuma nuna godiyarsu ga Gwamnan jihar da tawagarsa bisa halartar wannan biki, tare da nuna farin cikinsu ga sauran al’ummar da suka halarta.
