
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta tura allurar cutar mashaƙo guda 500,000 zuwa jihohin Katsina da Kano a wani yanayi na ɗaukar matakin gaggawa kan ɓarkewar cutar domin bayar da kariya acikin yara.
Ma’aikatar Lafiya da Walwalar Al’umma ta Tarayya ce ta sanar da haka a wata sanarwa da fitar a ranar Juma’a. Ta ce, Hukumar kula da lamuran Ci-gaban Lafiya a Matakin Farko ta Ƙasa (NPHCDA) ce ta gudanar da aikin raba allurar ne domin bayar da tallafin harkokin rigakafi a yankunan da al’amarin ya shafa.
Ma’aikatar ta ce, wannan ɓangare ne na bada agajin gaggawa da Ministan ma’aikatar, Farfesa Muhammad Ali Pate ya samar domin daƙile cigaba da yaɗuwar cutar da kuma ƙarfafa matakin kariya ga cutar a faɗin Nijeriya.
A cewar sanarwar, gwamnatin tarayyar ta kuma tura wata tawaga da ta ƙunshi haɗakar jami’an Cibiyar Kula da da bada Kariya ga Cututtuka ta Ƙasa (NCDC), NPHCDA, gwamnatocin jihohi da abokan hulɗar harkar lafiya na ƙasa-da-ƙasa.
Darakta-Janar na NCDC tare da daraktan lafiyar al’umma ne za su jagoranci kwamitin jami’an, wanda ya ƙunshi kwamishinonin lafiyan jihohin Katsina, Kano, Zamfara da Sakkwato. Haka kuma, akwai wakilan Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), UNICEF da na Shirin kula da Cutar Tarin Fuka da Mashaƙo a Jihar Katsina. Ma’aikatar ta bayyana cewa, an umarci kwamitin da ya gudanar da bincike musabbabin ɓarkewar cutar, ƙarfafa matakin sanya ido kan cutar da kuma wayar da kan jama’a a kai da yi wa yara rigakafi.
Kazalika, za a samar da damarmakin magance cutar a gundumomin Jihar Katsina uku, wato Katsina, Daura da Funtua da haɗin-gwiwar gwamnatin jihar don sauƙaƙe wa jama’ar da ta shafa damar magance cutar cikin sauƙi.
