
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Jumma’a aka kammala babban taron Ƙungiyar Maruwaita Labaran Wasanni ta Ƙasa (SWAN), inda aka sake zaɓa da rantsar da Mista Isaiah Kemje Benjamin (JP) da Amb. Ikenna Okonkwo ANIPR a matsayin shugaba da babban sakatare na wa’adin wasu shekaru uku.
Taron, wanda ya samu halartar wakilai daga jihohi a sassan Nijeriya, ya kuma samar da sabuwar majalisar zartarwar (NEC), wadda aka ɗora wa alhakin kula da harkokin ƙungiyar na tsawon shekaru uku.
Zaɓen, wanda aka gudanar a ranar 28 ga Agusta, 2026, ya bayar dama da kuma fage ga wakilai domin yin nazari akan goben ƙungiyar da kuma zaɓar jami’an da za su jagoranci harkokinta.
Duk da cewa da dama daga cikin muƙaman babu gasa akansu, an samu karawa a muƙaman mataimakin shugaba da mataimakin shugaba na shiyyar Arewa maso Gabas.
Ga jaddawalin zaɓaɓɓun jami’an SWAN, kamar yadda Leadership ta wallafa:
“President: Isaiah Kemje Benjamin (JP)
Deputy President: Nyong Bonny Silas
Secretary General: Ikenna Okonkwo
Deputy Secretary General: Samuel Ahmadu
Treasurer: Amusan Olufemi Ayorinde
Financial Secretary: Ijeoma Nwante
Vice President, North-East: Samuel Gangwaja
Vice President, North-West: Zaharadeen Saleh
Vice President, South-South: Azuka Chiemeka
Vice President, South-East: Ikemefuna Asika
Vice President, South-West: Ayodeji Ogunsakin.”
